Muna Tare da Dangote: ’Yan Najeriya Sun Kafe, Sun Ce Dole Gwamnati Ta Biyawa Dangote Bukata

Muna Tare da Dangote: ’Yan Najeriya Sun Kafe, Sun Ce Dole Gwamnati Ta Biyawa Dangote Bukata

  • ‘Yan Najeriya sun nuna goyon bayansu ga abin da Dangote ya sanya a gaba a matatarsa ta mai da ke Legas
  • Sun nemi tabbas a tabbatar da matatar ta fara aiki kuma an ba Dangote duk abin da yake bukata don ci gaba da aiki
  • Najeriya dai kasa ce da ta ke yin wani irin kasuwa na mai, inda ake kai danyen mai waje a kara siyo tatacce a dawo gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - ‘Yan Najeriya a kafar sada zumunta sun nemi gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da nasarar matatar mai ta Dangote.

A kwanan nan ne shugaban gamayyar kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ke kai koma da musayar miyau tsakaninsa da jami’an gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sauki zai zo nan kusa: Siminti zai sauka, BUA ya gano hanyar sauke farashi kayansa a Najeriya

'Yan Najeriya sun goyi bayan Dangote
Dangote muke yi: 'Yan Najeriya a rikicin Dangote da gwamnati | Hoto: Bass
Asali: Getty Images

Wannan musayar miyau dai ta fara ne kan matatar mai da Dangote ya gina da hanyar Ijebu zuwa Lekki a birnin Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar da ta shiga tsakanin Dangote da gwamnati

An samu hatsaniya a lokacin da hukumar kula da harkokin mai ta kasa NMDPRA ta yi tsokaci game da ingancin man da Dangote ke tacewa da kuma kitimurmurar da ke tattare da lasisin matatar.

A haka dai zantuka suka yi ta fitowa, ciki har da masu gargadin Dangote game da sanya kudadensa a fannin da ya shafi man fetur a Najeriya.

‘Yan Najeriya sun tsayawa Dangote

A kafar sada zumunta ta Twitter (X) aka samu matasa da dama da suka nuna goyon bayansu ga manufar samar da mai a gida daga matatar Dangote.

Gangamin #IStandWithDangote tuni ya yi kaurin suna a kafar, inda kow ake tofa albarkacin bakinsa game da kititmurmurar da ka tsakanin Dangote da jami’an gwamnati.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da suka jawowa gwamnatin Tinubu zanga zanga bayan shekara 1

A halin da ake ciki a Najeriya, babu abu daya da ke aiki daidai, don haka kusan kowanne matashi da ma masu shekaru a fusace ake.

Majalisa ta shiga tsakani a rikicinsu Dangote

A wani labarin, majalisar wakilan Najeriya ta yi shiga tsakani bayan rikicin da ya barke tsakanin gwamnatin tarayya da Dangote.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta zargi Dangote da rashin samar da ingantaccen mai a matarsa da ke Legas.

Daily Trust ta ruwaito cewa majalisar za ta gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki domin tantance gaskiyar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.