Gwamna Ya Ware N3.9bn Domin Siyo Motocin Alfarma? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna Ya Ware N3.9bn Domin Siyo Motocin Alfarma? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamnatin jihar Plateau ta fito ta yi martani kan zargin cewa ta ware N3.9bn domin siyo motocin alfarma a watanni uku na farkon shekarar 2024
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar wanda ya musanta zargin ya ce ko kaɗan ba a kashe waɗannan kuɗaɗen ba
  • Ya bayyana kuɗaɗen da aka ware domin siyo motocin wani ɗan ƙaramin kaso ne kawai na kasafin kuɗin shekarar 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta ƙaryata zargin da ake yi na cewa ta ware N3.9bn domin siyan motocin alfarma.

Kuɗaɗen dai waɗanda ke wakiltar kaso 47% na kuɗaɗen da za a kashe a jihar an ce an fitar da su ne a watanni uku na farkon shekarar 2024 domin siyo motocin.

Kara karanta wannan

Kwamishina ya fadi maƙudan kuɗin da gwamnatin Kano ke buƙata domin gyara makarantu

Gwamnatin Plateau ta musanta siyo motocin N3.9bn
Gwamnatin Plateau ta musanta ware N3.9bn domin siyo motocin alfarma Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Twitter

Gwamnatin Plateau ta musanta kashe N3.9bn

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Musa Ashoms, ya musanta rahotannin yayin da yake mayar da martani kan zargin, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya ce a zahiri, N3.9bn ɗin na daga cikin jimillar N152.8bn da aka ware domin kashewa a shekarar 2024, wanda hakan ne wakiltar kusan kaso 2.5% a watannin ukun farko na 2024, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Ya yi nuni da cewa rahoton da aka fitar a kafafen yada labarai akwai kura-kurai a cikinsa, inda ya ƙara da cewa kuɗaɗen da ka ware domin siyo motocin a watanni uku na farkon 2024, wani ɗan kaso ne kawai na kasafin kuɗin.

Gwamna Mutfwang ya gaji tsofaffin motoci

Kwamishinan ya bayyana cewa, a lokacin da Gwamna Caleb Mutfwang ya hau kan karagar mulki, ya gaji motocin da ba su aiki, inda ya ƙara da cewa gwamnatin da ta gabata ta tafi motocin da ke da lafiya.

Kara karanta wannan

An kashe mutane yayin da rigimar sarauta ta ƙara tsanani, hadimin gwamna ya yi magana

"Yawan hauhawar farashin kayayyaki ya yi tasiri sosai wajen siyan motocin, wanda ya tashi daga 24.66% a ƙarshen 2023 zuwa 33.9% a ƙarshen watanni ukun farko na 2024."
"Bugu da kari, farashin canji ya tashi daga N903 zuwa N1,600 kan kowace dala a cikin wannan lokaci, wanda ya yi matukar tasiri ga farashin kayayyakin da ake shigowa da su, ciki har da motoci."

- Musa Ashoms

APC ta fara zawarcin Gwamna Mutfwang

A wani labarin kuma, kun ji cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a shiyyar Arewa ta tsakiya sun fara tuntuba da zawarcin gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.

A cewar ƙusoshin jam'iyyar na shiyyar, jawo manyan mutane a jiki masu zuciya irinta Gwamna Mutfwang ya zama dole idan har APC na son sake karɓe jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng