Shirin Zanga Zanga Ya Samu Cikas Bayan Babbar Kungiya a Arewa Ta Fice, Ta Fadi Dalili

Shirin Zanga Zanga Ya Samu Cikas Bayan Babbar Kungiya a Arewa Ta Fice, Ta Fadi Dalili

  • Zanga-zangar adawa da halin ƙuncin da ake fama da shi a ƙasar nan ta gamu da cikas a jihar Zamfara bayan wata ƙungiya ta sanar da ficewarta
  • Ƙungiyar ƴan asalin jihar Zamfara ta ce ta ɗauki matakin janyewa daga zanga-zangar ne saboda rashin sanin ainihin shugabanninta
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa rashin sanin jagororin da za su jagoranci gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan na iya sanyawa ta rikiɗe ta koma tashin hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Kungiyar ƴan asalin jihar Zamfara (ZIEF) ta sanar da janyewa daga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne saboda rashin sanin haƙiƙanin shugabannin da za su jagoranci zanga-zangar a ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Minista ya yi magana mai kaushi, ya fadi kulla kullar da ake yi

Kungiyar ZIEM ta fasa zanga-zanga a Zamfara
Matasan Najeriya na shirin fitowa zanga-zanga a ranar, 1 ga watan Agusta Hoto: Anadolu Agency
Asali: Getty Images

Ƙungiyar ta bayyana cewa a bayyane yake a fili cewa zanga-zangar ta ƙasa ba ta da tsarin da ya dace domin tabbatar da cewa an gudanar da ita cikin lumana, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haƙan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Tanimu Abdullahi ya fitar a ranar Asabar.

Meyasa ƙungiyar ta fice daga zanga-zanga?

"A bisa rashin tsarin ingantaccen shugabanci da yadda za a gudanar da zanga-zangar, akwai yiwuwar zanga-zangar za ta iya rikiɗewa ta zama tashin hankali."
"Bayan tattaunawa da neman shawarwari daga wajen masu ruwa da tsaki, ƙungiyar ZIEF ta yanke shawarar janyewa daga zanga-zangar ƙasa da ke tafe domin hakan shi ne abin da ya fi alheri ga jihar Zamfara."
"Rashin sanin haƙiƙanin shugabanni da inda rashin sanin inda suka dosa ba ƙaramar barazana ba ce ga lafiyar mutane musamman a jihar Zamfara."

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi watsi da batun zanga zanga, ya fadi matakan da ya dauka

- Tanimu Abdullahi

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Malami ya shawarci matasan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani fitaccen malami ɗan ƙasar Sudan, Ambasada Al-Mustapha Bala Assudany, ya gargadi ƴan Najeriya musamman matasa da su guji yin zanga-zanga.

A wa'azin gabanin huduba a masallacin Sultan Bello Kaduna, malamin ya ja kunnen matasa da kada su baiwa makiyan kasar ƙofar da zasu ruguza Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng