Zanga Zanga: Babban Malamin Ƙasar Sudan Ya Aika Muhhimmin Saƙo Ga Matasan Najeriya

Zanga Zanga: Babban Malamin Ƙasar Sudan Ya Aika Muhhimmin Saƙo Ga Matasan Najeriya

  • Babban Malamin addinin Musulunci ɗan asalin kasar Sudan, Ambasada Al-Mustapha Bala Assudany ya roki ƴan Najeriya su janye zanga-zanga
  • Da yake wa'azin kafin huɗuba a Sultan Bello, malamin ya bayar da labarin abin da ya faru a Sudan wanda ya rikiɗe ya zama tashin hankali
  • Ya buƙaci matasan Najeriya su hakura kada su bari maƙiyan kasar nan su samu ƙofar da zasu shigo su tayar da tarzoma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Wani fitaccen malami ɗan kasar Sudan, Ambasada Al-Mustapha Bala Assudany, ya gargadi ‘yan Najeriya musamman matasa da su guji yin zanga-zanga.

Idan kuna biye damu kun san cewa ƴan Najeriya galibi matasa sun tsara fita zanga-zanga daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta domin nuna fushi kan ƙuncin rayuwa.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Minista ya yi magana mai kaushi, ya fadi kulla kullar da ake yi

Matasan Najeriya.
Babban Malamin Musulunci ɗan asalin ƙasar Sudan ya shawarci matasan Najeriya su janye zanga zanga Hoto: Anadolu
Asali: Getty Images

Gwamnati, malaman addini, sarakuna da sauransu sun roki matasa su haƙura su janye zanga-zangar, amma sun ce ba gudu ba ja da baya, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga: Assudany ya aika sako ga matasa

A wa'azin gabanin huduba a masallacin Sultan Bello Kaduna, malamin ya ja kunnen matasa da kada su baiwa makiyan kasar ƙofar da zasu ruguza Najeriya.

A matsayinsa na ɗan ƙasar Sudan, Sheikh Assudany ya dauki kimanin mintuna 20 yana faɗin abubuwan suka faru kafin da bayan zanga-zangar da ta kai ga yaki a kasar.

Ya ce a fakaice makiyan Najeriya suna tunzura matasan ne don su fito zanga-zangar kamar yadda suka yiwa ‘yan Sudan, wanda hakan ya janyo ɓarkewar yaƙi.

Malam Assudany ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su koyi darasi daga kasar Sudan domin kaucewa zubar da jini ko duk wani abu da ka iya kawo tashin-tashina.

Kara karanta wannan

JNI ƙarkashin Sarkin Musulmi ta roƙi alfarma daga wurin masu shirin yin zanga zanga

Ƙasasfen da zanga-zanga ta rusa

Ya lissafta kasashen Masar, Syria, Yemen, Libya, da Sudan a matsayin kasashen da suka ruguje sakamakon abin da ya fara daga zanga-zangar lumana, rahoton Arise tv.

Malamin ya ce:

"Kafin mu fara magana kan zanga-zangar da aka shirya a Najeriya, ta faru a wasu ƙasashen Musulmi Syria, Libya, Tunisia, Yemen, da Sudan. Ni dan kasar Sudan ne kuma abin da ya faru a Sudan shi ya faru a wasu kasashen musulmi.
"Matsin tattalin arziki ne dalilin zanga-zangar da aka yi a waɗannan ƙasashe. Abin da ya sa mutane suka yi zanga-zanga a Sudan, suna tunanin mafita za ta zo ta hanyar zanga-zanga."

Ministan Tinubu ya soki masu shirin zanga-zanga

A wani rahoton kuma ƙaramin ministan albarkatun ruwa, Muhammad Goronyo ya yi kakkausar suka ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ƙasar nan.

Ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da su nuna kishin ƙasa tare da ƙauracewa shiga zanga-zanga wacce a bayyana a matsayin ɓarna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262