Zanga Zangar Adawa da Tinubu: Minista Ya Yi Magana Mai Kaushi, Ya Fadi Kulla Kullar da Ake Yi
- Ƙaramin ministan albarkatun ruwa, Muhammad Goronyo ya yi kakkausar suka ga masu shirin gudanar da zanga-zanga ƙasar nan
- Ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da su nuna kishin ƙasa tare da ƙauracewa shiga zanga-zanga wacce a bayyana a matsayin ɓarna
- Ya nuna cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba wani daɗewa ta yi a kan mulki ba saboda haka tana buƙatar ƙarin lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Ƙaramin ministan albarkatun ruwa, Muhammad Goronyo, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi watsi da shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Ministan ya bukaci ƴan Najeriya musamman matasa da su ci gaba da yarda da tsarin Shugaba Bola Tinubu na kai ƙasar nan zuwa ga tudun mun tsira.
Muhammad Goronyo yayi magana ne a ranar Juma’a a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da gwamnatin jihar Sokoto ta shirya, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya caccaki shirin zanga-zanga
Ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su bari zanga-zangar da ake shirin yi ta sanya kishin da suke yiwa ƙasar nan ya ragu.
Ministan ya bayyana zanga-zangar da aka shirya a matsayin "ha'inci ne na siyasa", yana mai cewa hakan na iya jefa al'ummar ƙasar nan cikin halin rashin tsaro, rahoton jaridar New Telegraph ya tabbatar.
"Wannan gwamnati shekara ɗaya da wata biyu kawai ta yi daga cikin wa’adin mulkinta na shekaru huɗu. Ƴan Najeriya su kasance masu adalci da kishin ƙasa, su ba gwamnati lokaci domin ta yi abin da ya dace."
"Dole ne ƴan ƙasa masu kishi su haɗa kai domin daƙile wannan zanga-zangar ta ɓarna."
"Irin wannan yanayi ya haifar da ƙasashe kamar Sudan da Libya cikin koma bayan tattalin arziƙi mara misaltuwa, tare da durƙusar da kusan komai a ƙasashen."
- Muhammad Goronyo
APC ta ba masu shirya zanga-zanga shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC ta buƙaci masu shirya zanga-zangar da su yi watsi da ƙudirinsu na sanya matasa su fito kan tituna.
APC ta buƙaci masu shirya zanga-zangar da su yi watsi da yunƙurinsu na ganin Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da kundin tsarin mulkin shekarar 1999.
Asali: Legit.ng