'Bom' Ya Tarwatse da Motar Dakarun Sojoji, An Rasa Rayuka da Yawa a Arewa

'Bom' Ya Tarwatse da Motar Dakarun Sojoji, An Rasa Rayuka da Yawa a Arewa

  • Bom ya tashi da motar sojoji yayin da suke hanyar zuwa kauyen Kukawa da safiyar ranar Alhamis a jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa duka sojoji bakwai da ke cikin motar sun mutu sakamakon fashewar bam ɗin a daidai kauyen Bawarti
  • Wasu majiyoyi guda biyu sun ɗora alhakin wannan hari kan kungiyar ƴan tada kayar baya ISWAP, wacce ta fi ƙarfi a yankin tafkin Chadi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Wata nakiya ta fashe a karkashin motar dakarun sojojin Najeriya inda ta kashe sojoji bakwai a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.

Jihar Borno dai na ɗaya daga cikin jihohin da ƙungiyar ƴan tada kayar baya da ke ikirarin jihadi Boko Haram ta yiwa illa tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari Masallaci, sun kashe bayin Allah

Sojojin Najeriya.
Abun fashewa ya tashi da motar jami'an tsaro, sojoji 7 sun mutu a Borno Hoto: Nigerian Army
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa sojojin suna kan hanyar zuwa kauyen Kukawa a lokacin da motarsu ta taka abun fashewar wanda ake kyautata zaton bom ne da safiyar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bom.ya halaka sojoji 7

Wasu majiyoyi daga rundunar ƴan banga da suka nemi a sakaya bayanansu sun tabbatar da aukuwar lamarin.

"Duka sojoji bakwai da ke cikin motar sun mutu sakamakon tashin bam ɗin a kauyen Bawarti," in ji jagoran yan banga masu yaƙar ƴan tada kayar baya Babakura Kolo.

Sai dai dukkan majiyoyin guda biyu sun ɗora alhakin wannan harin kan kungiyar ta'addancin ISWAP, wanda ta ɓalle daga Boko Haram.

Yadda Arewa ke fama da matsalar tsaro

Sama da shekaru goma da suka wuce dakarun sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro ke ci gaba da yaƙi da ƴan tada ƙayar baya a yankin.

Kara karanta wannan

Wani abin fashewa da ake zargin 'bam' ne ya tarwatse a fitacciyar kasuwa a Arewa

Kimanin mutane 40,000 ne aka kashe tare da raba mutane miliyan biyu da muhallansu a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Duk da ana ganin zaman ƙafiya ya fara dawowa a 'yan watannin nan, amma har yanzu ISWAP da kungiyar Boko Haram na kai hare-hare kan ayarin motocin sojoji da fararen hula.

A yanzu ana zargin ISWAP ce ta dasa bam ɗin da ya tashi da motar sojoji har ya kashe dakaru bakwai a Borno, Reauter ta kawo a rahoton da ta wallafa.

Yan bindiga sun farmaki masallaci

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kashe mutane biyar a cikin masallacin kauyen Katakpa da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa.

Rahotanni daga mazauna kauyen sun nuna cewa waɗanda maharan suka kashe sun gudo ne daga garuruwansu saboda yawaitar hare-hare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262