Rabiu Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi a Najeriya
- Kwankwaso ya roƙi masu shirya zanga-zanga sun duba sakamakon da zai biyo baya kamar asarar rayuka da dukiyoyi
- Jagoran NNPP na ƙasa ya roƙi ƴan Najeriya su yi amfani da ƙarfin kurinsu wajen sauya duk shugaban da ya masu ba daidai ba
- Rabiu Kwankwaso ya ce ya fahimci halin da ƴan Najeriya ke ciki amma duk da haka ba zanga zanga ce mafita ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsokaci kan zanga zangar da matasa ke shirin yi a faɗin ƙasar daga ranar 1 ga watan Agusta.
Kwankwaso ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun tsinci kansu a kuncin rayuwa saboda kuskuren shugabanni tun 2007 amma duk da haka ya ce akwai damar gyara.
Ya ce zanga-zangar da matasa ke shirin yi ta ƙara nuna ɓacin ran da mutane ke ciki da kai su bango saboda halin da suka shiga da kuma fatan ganin Najeriya ta gyaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X da safiyar yau Asabar, 27 ga watan Yuli, 2024.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a 2023 ya roƙi ƴan Najeriya su sa kishin ƙasa a gaba, sannan su ƙara hakuri su baiwa gwamnati goyon baya domin ta samu nasara.
Zanga-zanga: Kwankwaso ya faɗi mafita
Ya shawarci matasa su ƙara hakuri, inda ya ce maimakon zanga-zanga suna da damar canza duk shugaban da ya gaza ta hanyar amfanu da kuri'unsu a akwatun zaɓe.
Kwankwaso ya gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga, yana mai cewa hakan na iya jawo tada zaune tsaye da tsahin hankalin da asarar rayuka da dukiyoyi.
"Na. fahimci damuwarku da kuma burin kawo sauyi, duk da haka ina roƙon ku duba sakamakon da ka iya biyo bayan zanga-zangar ƙasa, maimakon haka ku bi hanyar da ta dace wajen kawo canji, ku yi amfani da karfin kuri'unku.
Wani ɗan Kwankwasiyya, Mus'ab Abdullahi ya ce yana zargin wasu daga sama ne suka sa Kwankwaso ya juyawa zanga-zangar nan baya saboda ya san yana kaunar talakawa.
Mus'ab ya shaidawa Legit Hausa cewa zanga zanga ba fashi saboda abubuwan da ake a ƙasar nan ya yi yawa kuma cewarsa Kwankwaso ya ambaci wasu daga ciki.
"Idan ka duba maganganun Kwankwaso, shi kansa ya faɗi wasu abubuwan rashin adalci da gwamnati ta yi, ba su kenan ba, don haka muna ganin girmansa amma dai za mu fita zanga-zanga," in ji shi.
Uba Sani ya gana da shugabannin tsaro
A wani rahoton Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya fara ɗaukar matakai da nufin hana zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta mai zuwa.
Sanata Uba Sani ya gana da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, su roki su wayar kan mutane kan illar zanga-zanga.
Asali: Legit.ng