Tsadar Rayuwa: Kashim Shettima Ya Ba 'Yan Najeriya Mafita Maimakon Yin Zanga Zanga
- Mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima ya rashin gamsuwarsa da shirin gudanar da zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan
- Kashim Shettima wanda ya amince cewa ƴan Najeriya na cikin halin ƙunci ya yi nuni da cewa yanzu ba lokacin da ya kamata a gudanar da zanga-zanga ba ne
- Ya bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu, lokaci ne na magance matsalolin da suka addabi ƙasar nan maimakon fitowa kan tituna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Ƙashim Shettima ya nuna muhimmancin ɗaukar matakan da suka dace maimakon fitowa kan tituna domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya fitar a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne wajen ƙaddamar da shirin kiwon lafiya na GCNg wanda ke ƙoƙarin kawar da matsalar tamowa da ƙarancin abinci a Najeriya.
Me Kashim Shettima ya ce kan zanga-zanga?
"Wannan lokaci ne da za mu magance matsalolinmu, ba mu yi zanga-zanga ba. Akwai ƴancin yin zanga-zanga a kusan dukkanin inda ake mulkin dimokuraɗiyya a duniya."
"Amma idan za ka fara zanga-zanga sannan ba ka san inda za ta ƙare ba, wannan hanyar kama-karya ce."
"Mun yarda ƴan Najeriya na cikin halin ƙunci kuma muna tausaya musu. Da an fara girbi, mun yi amanna cewa talaka zai samu sauƙi."
- Kashim Shettima
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Minista ya lallashi 'yan zanga zanga, Wike ya yi alkawari shugaba Tinubu zai kawar da yunwa
- Gwamnan APC ya tsure, ya bayyana fargabarsa a kan shirin zanga zangar lumana
- 'Yan majalisa sun ba Tinubu mafita kan zanga zangar da ake shirin yi
Gwamnatin Tinubu ba ta son zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana dalilin da ya sanya ba ta so a gudanar da zanga-zanga a ƙasar nan.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Mohammed Idris, ya ce ko kaɗan gwamnatin ba ta so matasa su fito kan tituna domin yin zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng