'Yan Sanda Sun Yi Tuni Kan Haramcin Gudanar da Zanga Zanga a Jihar Arewa
- Ƴan sanda a jihar Borno sun fitar da saƙpm gargaɗi ga mutanen jihar kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan
- Rundunar ƴan sandan jihar ta gargaɗi jama'a kan shiga cikin zanga-zangar wacce za a fara gudanarwa a faɗin ƙasar nan daga ranar 1 ga watan Agusta
- Rundunar ta bayyana cewa har yanzu akwai dokar ta ɓaci a kan rashin tsaro a jihar wacce ta haramta yin gangamin jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Rundunar ƴan sandan Borno ta gargaɗi mutanen jihar da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan.
Rundunar ƴan sandan ta aika da saƙon jan kunnen ne ga mutanen jihar a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2024.
Doka ta haramta zanga-zanga a Borno
Rundunar ta bayyana cewa dokar ta ɓaci kan rashin tsaro da ke ci gaba da aiki a Borno kai tsaye ta haramta gudanar da zanga-zanga, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Nahum Daso, wacce ya fitar a madadin kwamishinan ƴan sanda, Yusufu Mohammed.
Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa ta na sane da cewa wasu “wasu marasa kishin ƙasa" na tattaro matasa domin gudanar da zanga-zanga mai taken #EndbadgovernmentinNigeria2024 ta kafafen sada zumunta da sauran wurare.
"Jama’a su lura cewa har yanzu jihar Borno na cikin dokar ta-ɓaci, domin haka har yanzu dokar hana yin gangamin jama’a a jihar tana nan daram."
- ASP Nahum Daso
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa rundunar tana haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin daƙile duk wani yunƙuri na take doka da oda.
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Minista ya lallashi 'yan zanga zanga, Wike ya yi alkawari shugaba Tinubu zai kawar da yunwa
- Gwamnan APC ya tsure, ya bayyana fargabarsa a kan shirin zanga zangar lumana
- 'Yan majalisa sun ba Tinubu mafita kan zanga zangar da ake shirin yi
Gwamna Zulum ya magantu kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ba al'ummar Borno da ƴan Najeriya baki ɗaya shawara kan zanga-zangar da ake shirin yi.
Gwamnan na jihar Borno ya buƙace su da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a wata mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng