Zanga Zanga: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule da Gwamnonin APC, An Samu Bayanai
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gayyato gwamnonin jam'iyyar APC domin tattaunawa a fadar Aso Villa da ke Abuja
- Bola Tinubu ya sanya labule da gwamnonin jihohin ne yayin da matasa ke ci gaba da shirin fitowa kan tituna domin yin zanga-zanga
- Ganawarsu ba za ta rasa nasaba da nemo hanyoyin hana aiwatar da zanga-zangar ba, matasa sun fusata da halin ƙuncin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wasu gwamnonin jam'iyyar APC a fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja.
Taron ya biyo bayan dakatar da zaman majalisar zartaswa ta ƙasa da aka shirya yi a ranar Alhamis, 25 ga watan Yulin 2024.
Gwamnonin jihohi sun gana da Tinubu
Jaridar Nigerian Tribune ta ce gwamnonin sun isa fadar shugaban ƙasan ne a cikin wata zungureriyar mota ƙirar Coaster da misalin ƙarfe 1:20 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma shi ne ya jagoranci gwamnonin zuwa ofishin shugaban ƙasa tare da shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Gwamna Abdulrazaq Abdulrahman na jihar Kwara.
Daga cikin mahalarta taron akwai mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, Gwamna Bassey Otu na jihar Cross Rivers, Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi da sauransu.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, ministan kuɗi Wale Edun da ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu na daga cikin mahalarta taron, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Taron na zuwa ne bayan a jiya Laraba, gwamnonin Najeriya sun gudanar da na su taron a Abuja.
Meyasa Tinubu ya kira taron?
Duk da cewa ba a bayyana abin da za a tattauna a wajen taron ba, amma ba zai rasa nasaba da wahalhalun da ake fama da su a ƙasar nan ba da kuma ƙoƙarin ganin al'amura sun daidaita.
Gwamnatin tarayya kuma tana ƙoƙarin ganin ta daƙile zanga-zangar da matasa ke shirin yi domim nuna adawa da tsadar rayuwa da halin ƙuncin da ake fama da shi a ƙasar nan.
Bisa ga dukkan alamu waɗannan batutuwan su ne abin da taron zai mayar da hankali a kansu.
Tinubu: Jigon APC ya roƙi ƴan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC, Uche Nwosu, ya roƙi ƴan Najeriya da su ba Shugaba Bola Tinubu lokaci tare da fasa yin zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Uche Nwosu ya bayyana cewa babu adalci ko kaɗan a yi tsammanin cewa gwamnatin da ta yi shekara ɗaya a kan mulki za ta gyara ɓarnar da aka kwashe shekaru ana yi a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng