An Rasa Rayukan Mutum 5 Bayan Gini Ya Rufto Kan Ma'aikata
- Wani ginin da ake aikin ginawa ya rufto a unguwar Maryland da ke Legas a yankin Kudu maso Yamma na Najeriya
- Ginin da ya rufto da sanyin safiyar ranar Alhami, 25 ga watan Yulin 2024, ya yi sanadiyyar rasuwar mutum biyar waɗanda duk masu aikin ginin ne
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce an samu nasarar ceto wasu mutum biyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Mutum biyar sun rasu sakamakon ruftawar wani gini da ke lamba 13, kan titin Wilson Mba, a unguwar Maryland da ke Legas.
Ginin wanda ake aikin ginawa ya ruguje ne da misalin ƙarfe 3:49 na safiyar ranar Alhamis a unguwar Maryland da ke jihar Legas a Najeriya.
Me hukumomi suka ce kan ruftowar ginin?
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban na hukumar LASEMA ya ce an ceto mutane biyar waɗanda dukkansu maza ne da ransu daga wurin da ginin ya ruguje.
Ya bayyana cewa an garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
"Hukumar LASEMA ta kai ɗauki zuwa wajen da lamarin ya auku inda ta gano cewa ginin wanda ake aikin ginawa ya ruguje."
"Nan da nan aka fara aikin ceto waɗanda suka maƙale a cikinsa. An gano gawarwakin maza mutum biyar yayin da aka ceto maza mutum huɗu, sannan an ceto wani namiji ɗaya da ya maƙale a ƙarƙashin ɓuraguzan ginin."
"Dukkanin mutanen masu aikin gini ne. An ba su kulawa kafin daga bisani aka wuce da su zuwa asibiti."
- Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu
Masallaci ya rufto a Legas
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutane da dama sun rasu bayan wani masallaci ya rufto kan masallata a Legas ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu.
Ginin ya rufto kan masallatan ne da rana a unguwar Papa Ajao a jihar Legas wacce sau tari ake samun rugujewar gine-gine.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng