"Mun Gano Wata Maƙarƙashiya," Sojoji Sun Aika Saƙo ga Masu Shirin Yin Zanga Zanga

"Mun Gano Wata Maƙarƙashiya," Sojoji Sun Aika Saƙo ga Masu Shirin Yin Zanga Zanga

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi masu shirya zanga-zanga a wata mai zuwa su kauracewa duk abin da zai kawo tada zaune tsaye
  • Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya ce sojoji sun gano maƙarƙashiyar da ake shiryawa da sunan zanga-zanga
  • Manjo Janar Edward Buba ya ce dakarun sojoji ba za su naɗe hannu suna kallo a jawo fitina a ƙasar nan irin wadda ta afku a ƙasar Kenya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta gargaɗi jagororin da ke shirin yin zanga-zanga su gujewa duk wani abu da zai kawo tada zaune tsaye a ƙasar nan.

Sojojin sun yi wannan gargaɗin ne a lokacin da ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga ta tsawon kwanaki 10 daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana jihar Arewa da ba za a yi zanga zanga ba

Babba hafsan tsaro, Christopher Musa.
Rundunar sojoji ta gargaɗi matasan da ke shirin yin zanga zanga a Najeriya Hoto: @DefenceHQ
Asali: Facebook

Daraktan sashen yaɗa labarai na hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Alhamis, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Janar Buba ya ce dakarun sojoji ba za su zuba ido suna kallo tashe-tashen hankula su ɓarke a Najeriya ba, rahoton Daily Trust.

Manufar masu shirya zanga-zanga a Najeriya

Sojan ya yi nuni da cewa alamu sun nuna manufar masu shirya wannan zanga zanga ita ce su jawo bala'i irin wanda ya auku a zanga-zangar da ta faru a ƙasar Kenya.

Janar Buba ya ce duk da cewa mutane na da ‘yancin bayyana kokensu, amma sojoji ba za su lamunci duk wata kalar tarzoma ko zanga-zanga ba.

Ya ƙara da cewa rundunar sojoji ta gano maƙarƙashiyar da wasu ɓata-gari ke shiryawa ta hanyar sajewa da masu zanga-zanga da kai farmaki kan mutane.

Kara karanta wannan

Gwamnonin jihohi 36 sun yi magana kan zanga zangar da matasa ke shirin yi

"Duk da ƴan kasa suna da ƴancin gudanar da zanga-zangar lumana amma ba su da ikon shirya gangamin da zai kawo tada zaune tsaye da ta'addanci.
"A bayyane yake wannan zanga-zangar da aka shirya tana kama da tashe-tsahen hankulan Kenya wanda ya zama alaƙalai kuma har yanzu ba a warware shi ba.
"Don haka hukumomin soji ba za su tsaya suna kallo fitina ta faɗawa ƙasar nan ba saboda mun ga illar yaƙi da tashin hankali a ƙasashe da dama da aka tura mu wanzar da zaman lafiya."

- Manjo Janar Edward Buba.

Gwamnoni sun magantu kan zanga-zanga

Ku na da labarin ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi magana kan al'amuran tsaro musamman zanga-zangar da matasa ke shirin yi.

Gwamnonin sun bayyana cewa sun samu bayani daga ofishin Nuhu Ribadu kan zanga zanga kuma ya yi alƙawarin taimaka masu wajen samar da tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262