'Yan Majalisa Sun ba Tinubu Mafita Kan Zanga Zangar da Ake Shirin Yi
- Marasa rinjaye na majalisar wakilai sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da masu shirya gudanar da zanga-zanga a ƙasar nan
- Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya buƙaci gwamnati da ta share musu hawaye kan buƙatun da suke nema
- Ya bayyana cewa ko kaɗan ba su goyon bayan gudanar da zanga-zanga saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu sassan ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƴan majalisar wakilai na jam'iyyun adawa buƙaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da masu shirya zanga-zangar da za a yi a faɗin ƙasar nan tare da biya musu buƙatunsu.
Ƙungiyoyi daban-daban sun yi kira da a gudanar da zanga-zanga tun daga ranar 1 ga watan Agusta, domin nuna adawa da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.
Wace shawara ƴan majalisa suka ba Tinubu?
A ranar Laraba, 24 ga watan Yuli, marasa rinjaye na majalisar wakilai sun buƙaci gwamnatin Shugaba Tinubu da ta magance matsalolin da masu zanga-zangar suke neman a shawo kansu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na daga cikin matsayar da ƴan majalisar suka cimma a ƙarshen taron liyafar cin abincin dare a da suka yi a birnin tarayya Abuja, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Meyasa ba su son a yi zanga-zanga
Da yake zantawa da manema labarai shugaban marasa rinjayen, Kingsley Chinda, ya buƙaci a fasa zanga-zangar musamman ganin yadda ake fama da rashin tsaro a wasu sassan ƙasar nan.
"Muna kira ga gwamnati da ta tattauna da masu shirin yin zanga-zangar da kuma yin duba kan buƙatun da suke nema musamman ɓangarorin da ke buƙatar sa hannun gwamnati."
"Ya kamata gwamnati ta shiga tsakani tare da tabbatar da cewa an warware matsalolin cikin ruwan sanyi."
"Ba za mu goyi bayan zanga-zanga ba saboda a baya mun ga yadda bara-gurbi suke yin kutse cikin zanga-zangar lumana domin tayar da hankali."
- Kingsley Chinda
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Zanga-zangar adawa da Tinubu: Jam'iyyar APC ta ɗauki muhimmin mataki
- Tsohon kakakin kamfen PDP ya mayar da martani mai zafi ga Atiku kan zanga-zanga
- Gwamnatin Tinubu ta fadi hanyar magance zanga zangar da ake shirin yi
Gwamnatin Tinubu ba ta son zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana dalilin da ya sanya ba ta so a gudanar da zanga-zanga.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Mohammed Idris, ya ce ko kaɗan gwamnatin ba ta so matasa su fito kan tituna domin yin zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng