Gwamnoni da Wasu Ministoci Sun Fara Ƙoƙarin Hana Matasa Zanga Zangar da Suke Shirin Yi
- Gwamnonin jihohin Najeriya da wasu ministoci za su gana da nufin lalubo hanyar hana faruwar zanga-zangar da matasa ke shirin yi
- Hakan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka a taron George Akume da duka ministoci ranar Laraba a Abuja
- Wata majiya ta bayyana batutuwan da taron ya mayar da hankali da kuma shawarwarin da aka gabatar domin hana zanga-zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce a shirye ta ke ta tattauna da waɗanda suka shirya yin zanga-zanga a fadin kasar nan daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
A taron gaggawar da aka yi ranar Laraba, gwamnati ta umarci duka ministoci su koma gida a jihohinsu daga ranar 24 ga Yuli zuwa ranar da aka shirya fara zanga zanga.
Gwamnoni za su gana da ministoci
Punch ta tattaro cewa gwamnatin tarayya ta kuma zabi wasu ministoci domin su gana da gwamnonin jihohi 36 a taron majalisar tattalin arziki (NEC) wanda za a yi yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na ɗaya daga cikin shawarwarin da aka amince da su a wurin ganawar sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da ministoci a Aso Villa, rahoton The Nation.
Wata takarda da ta fito daga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ta nuna cewa tsohon ministan matasa da wasanni, Sunday Dare na cikin waɗanda aka gayyata.
Gwamnatin Tinubu ta ɗauki shawarwari
Duk da ba a bar ƴan jarida sun shiga ɗakin taron ba, amma wasu majiyoyi sun ce zanga-zangar da ake shirin yi na ɗaya daga cikin abubuwan da aka tattauna a kai.
"Duka ministoci sun halarci taron, sun ba da shawarar a fito a yi wa ƴan ƙasa jawabi kuma in da hali shugaban ƙasa ya kamata ya yi da kansa, amma sai an sanar da Tinubu tukunna.
"An buƙaci kowane minista ya kawo muhimman ayyuka uku da ya yi nasarar kammalawa a shekara ɗaya, za a haɗa su duka a sanar da ƴan Najeriya.
"A taƙaice dai gobe (yau Alhamis) ministan kuɗi zai kira taron manema labarai ya faɗi halin da tattalin arziki ke ciki, amma sauran nasarorin za a haɗa su a gabatar a lokaci na daban," in ji wata majiya.
Bwala ya maida martani ga Atiku
A wani rahoton kuma Daniel Bwala ya caccaki tsohon mai gidansa Atiku Abubakar kan zanga-zangar da matasa ke shirin gudanarwa a watan Agusta.
Tsohon kakakin kamfen Atiku ya ce zanga-zangar ba ta zama dole ba domin shugaban ƙasa na iya bakin ƙoƙarinsa wajen yayewa ƴan Najeriya damuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng