Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Hanyar Magance Zanga Zangar da Ake Shirin Yi
- Gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu shirin fitowa kan tituna da niyyar yin zanga-zanga su kwantar da hankulansu
- Gwamnatin ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da ministocinsa na aiki tuƙuru domin ganin sauƙi ya samu a ƙasar nan
- Ministan yaɗa labarai wanda ya bayyana hakan, ya ce zanga-zangar lamari ne na cikin gida wanda za a warware domin a samu ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta yi kira ga masu shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan saboda matsalar karancin abinci da yunwa, da su kwantar da hankalinsu.
Gwamnatin ta buƙace su da su rungumi zaman lafiya, tana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da ministocinsa na ƙoƙarin sauya lamarin.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta tarayya a Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya jaddada cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin warware matsalolin da ake fuskanta, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Me gwamnatin Tinubu ta ce kan zanga-zanga?
Mohammed Idris ya bayyana zanga-zangar da aka shirya a matsayin "lamarin cikin gida" wanda za a warware domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.
"Waɗanda suke son yin zanga-zanga ƴan uwanmu ne. Wannan lamari ne da ya shafi Najeriya, kuma muna lura da shi da kyau, muna fatan za a samu zaman lafiya."
"Shugaban ƙasa da sauran manyan jami'an gwamnati suna ta ganawa da masu ruwa da tsaki. Wannan ita ce ƙasa ɗaya tilo da muke da ita, kuma mun yi amanna cewa Najeriya za ta gyaru.
Shugaban ƙasa da ministocinsa suna aiki tuƙuru. Dukkanmu muna saurare, kuma saƙon shugaban ƙasa kodayaushe shi ne ku kwantar da hankali ku ƙara mana lokaci. Za a magance dukkanin buƙatun ku."
- Mohammed Idris
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Zanga zanga: Tsohon Ministan Buhari ya fadawa matasa hadarin hawa tituna
- Ana harin fara zanga zanga, Sufeto Janar na 'Yan Sanda ya aika da sako mai zafi
- Atiku ya yi magana kan zanga zanga, ya aika sako mai zafi ga Tinubu
Jigon APC ya ba ƴan Najeriya shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam’iyyar APC a jihar Ondo, Dakta Femi Adekanmbi, ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin yi.
Jigon na APC ya yi kira ga matasan Najeriya da su janye zanga-zangar da suke shirin yi a fadin ƙasar nan saboda halin ƙuncin da ake ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng