Jigon APC Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yiwa Tinubu Yayin da Ake Harin Zanga Zanga

Jigon APC Ya Fadi Abin da Ya Kamata a Yiwa Tinubu Yayin da Ake Harin Zanga Zanga

  • Wani babban jigo a jam'iyar APC a jihar Ondo ya buƙaci matasa da su haƙuri daga shiga zanga-zangar da ake shiryawa a faɗin ƙasar nan
  • Dakta Femi Adekanmbi ya buƙaci a ƙarawa shugaban ƙasa Bola Tinubu lokaci ya cika alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe
  • Kiran na sa dai na zuwa yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da yin haramar fitowa kan tituna domin nuna adawa da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Wani jigon jam’iyyar APC a jihar Ondo, Dakta Femi Adekanmbi, ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan.

Jigon na APC ya yi kira ga matasan Najeriya da su janye zanga-zangar da suke shirin yi a fadin ƙasar nan saboda halin ƙuncin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi barazanar maka hadimin Tinubu a kotu, ya fadi dalilin neman diyyar N5bn

Jigon APC ya ba 'yan Najeriya shawara
Jigon APC ya bukaci matasa kada su yi zanga-zanga Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Amfanin fasa zanga-zangar adawa da Tinubu

Dakta Adekanmbi wanda tsohon kwamishina ne na ayyuka na musamman, al’adu da yawon bude ido a jihar, ya bayyana cewa fasa zanga-zangar zai samar da zaman lafiya, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a birnin Akure, babban birnin jihar a ranar Laraba.

Adekanmbi ya yi kira ga matasa da su ba gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu damar aiwatar da manufofinsa na kawo sauyi ga ƙasar nan.

Jigon APC ya ba matasa shawara

Jigon na APC ya jaddada buƙatar yin haƙuri da gwamnati, inda ya buƙaci matasa da su bar Shugaba Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zabe domin kawo sauyi mai kyau a Najeriya.

"Tinubu ya nuna da ƙwarewa da niyyar tunkarar ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya dauki zafi kan zanga zanga, ya fadi dalilin shiryata

"Mu ba shi dama ya kawo sauyi. Yana da tsarin farfaɗo da Najeriya. Tare da goyon bayanmu, ina da yaƙinin zai yi abin da ya dace."

- Femi Adekanmbi

Wike ya fusata kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya nuna rashin jin dadinsa game da shirin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan.

Wike wanda ya yi magana a ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024, ya bayyana zanga-zangar da aka shirya yi a watan Agusta a matsayin wacce za a yi saboda siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng