An Tona Yadda Bata Gari Ke Shirin Kai Hari Gidan Gwamnati da Sunan Zanga Zangar Lumuna

An Tona Yadda Bata Gari Ke Shirin Kai Hari Gidan Gwamnati da Sunan Zanga Zangar Lumuna

  • Wata kungiyar matasa a Kogi ta yi kakkausan lafazi kan zargin shirin kai hari gidan gwamnatin jihar a lokacin zanga zanga
  • Rahotanni sun nuna cewa an yi zargin kai harin ne bisa tunanin cewa tsohon gwamna Yahaya Bello na boye a gidan gwamnatin
  • Kungiyar matasan ta zargi yan siyasar da suka fadi zabe da kitsa lamarin domin tayar da tarzoma da kawo ci baya a jihar Kogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Wata kungiyar matasa a jihar Kogi ta ce akwai barazanar kai hari ga gidan gwamnati a lokacin zanga zanga.

Matasan sun ce akwai yan siyasa da suke neman tayar da fitina a jihar bayan sun gaza tabuka komai a lokutan zabukan 2023.

Kara karanta wannan

Fusatattun dalibai sun babbake gidan shugaban kwaleji a Arewa, bayanai sun fito

Gwamnan Kogi
Ana zargin kai hari gidan gwamnatin Kogi a lokacin zanga zanga. Hoto: Alhaji Usman Ahmed Ododo
Asali: Facebook

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa matasan sun fadi babban dalilin da ya sa ake shirin kai hari ga gidan gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kai hari gidan gwamnati da zanga-zanga

Kungiyar matasan ta bayyana cewa yan siyasa na zargin cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya buya a gidan gwamnatin jihar.

A cewar matasan, saboda haka ne aka shirya makircin amfani da zanga zangar domin kai masa hari.

Gwamnatin Kogi za ta zauna kan shiri

Daily Post ta wallafa cewa kungiyar matasan ta bayyana cewa duk wanda ya yi yunkurin kai harin zai sha mamaki fiye da yadda yake tsammani.

Kungiyar ta fadi haka ne domin cewa gwamna Usman Ahmed Ododo da tsohon gwamna Yahaya Bello suna daidai da duk wani mai tada fitina.

Shugaban kungiyar, Tunde G. Muhammed ya ce ba za su yarda da duk wani kokari kan mayar da dimokuraɗiyya baya a jihar ba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Tunde G. Muhammed ya ce maganar kama Yahaya Bello kuma tana gaban alkali saboda haka bai kamata a mata katsalandan ba.

Tinubu ya yi magana kan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu yayi kira ga matasa da su hakura da fitowa zanga-zanga da suke niyya kan yunwa da matsin rayuwa.

Shugaba Bola Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a Abuja yayin da ya gana da majalisar sarakunan gargajiya ta Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng