APC Ta Fallasa Masu Shirya Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu

APC Ta Fallasa Masu Shirya Zanga Zangar Adawa da Gwamnatin Tinubu

  • Jam'iyyar APC ta gargaɗi ƴan Najeriya da kada su shiga zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Shugaban jam'iyyar na Rivers, Cif Tony Okocha, ya yi zargin wasu ƴan siyasa ne da suka gaza kataɓus a ƙasar nan suke shirya zanga-zangar
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da marawa gwamnatin Shugaba Tinubu baya domin yana niyya mai kyau ga ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta gargaɗi ƴan Najeriya kan yin zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

APC ta bayyana cewa zanga-zangar shiri ne na wasu ƴan siyasa da suka kasa yin kataɓus a ƙasar nan.

APC ta fallasa masu shirya zanga-zanga kan Tinubu
APC ta zargi 'yan siyasa da shirya zanga-zanga kan Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

APC ta fallasa masu shirya zanga-zanga

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan zanga zanga, ya aika sako mai zafi ga Tinubu

Shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar Rivers, Cif Tony Okocha ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa a Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tony Okocha ya gargaɗi ƴan Najeriya kan shiga cikin zanga-zangar da ya bayyana a matsayin aikin ƴan siyasa da aka daina yayinsu.

Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da nuna goyon bayansu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Matsayar APC kan zanga-zanga

"A matsayinmu na jam’iyya a jihar Rivers kuma ƴan Najeriya masu kishin ƙasa, za mu so mu yi amfani da wannan damar domin gargaɗi kan zanga-zangar da mutanen da na ke kira ƴan siyasa da suka gaza suka shirya."
"Ba za su iya ruguza jam’iyyar APC ko shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba. Ya kamata mu marawa shugaban ƙasa baya domin ya ƙudiri aniyar ciyar da Najeriya gaba. Zai ɗauki lokaci, amma za a yi nasara."

Kara karanta wannan

Ana harin fara zanga zanga, Sufeto Janar na 'Yan Sanda ya aika da sako mai zafi

"Ka da mu kwatanta Najeriya da Kenya ko Sudan. Yanayinsu ya bambanta kuma ba za a iya kwatanta yawanmu da waɗancan ƙasashen ba. Goyon bayan zanga-zangar zai haifar da hargitsi ne kawai."
"Muna ba ƴan Najeriya shawara da kada su shiga zanga-zangar ko goyon bayan abin da na kira ƴan siyasa da suka gaza waɗanda suke ganin za su iya ruguza jam’iyyar APC ko shugaban ƙasa."

- Cif Tony Okocha

Atiku ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa ƴancin ƴan ƙasa na yin zanga-zanga yana cikin kundin tsarin mulkin Najeriya domin suna da ƴancin yin hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng