Atiku Ya Yi Magana Kan Zanga Zanga, Ya Aika Sako Mai Zafi Ga Tinubu
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga
- Atiku ya bayyana cewa masu son tauye ƴancin yin zanga-zanga a yanzu, su ma sun jagoranceta a shekarar 2024
- Ya yi gargaɗin cewa hana mutane fita tituna domin nuna adawarsu kan halin da ake a ƙasar nan, zai zama yin karan tsaye ga kundin tsarin mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa ƴancin ƴan ƙasa na yin zanga-zanga yana cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa kan zanga-zangar a shafinsa na X a ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu da ta tsaya ta yi abin da ya dace.
Me Atiku ya ce kan zanga-zanga?
Jigon na jam'iyyar PDP ya ce dole ne gwamnati ta samar tsaro ga ƴan ƙasa domin su yi amfani da yancin da kundin tsarin mulki ya ba su na yin zanga-zangar lumana.
"A bayyane yake cewa ƴan Najeriya, ciki har da magoya bayan Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki, sun shiga cikin yunwa, fushi da rashin tabbas wanda wannan gwamnati mara kan gado ta jefa su a ciki."
"Abin ban mamaki ne cewa waɗanda a yanzu ke neman tauye waɗannan haƙƙokin su ne suka jagoranci zanga-zanga a shekarar 2012."
"Gwamnatin da ta san abin da take yi, za ta tabbatar da tsaro da yanayi mai kyau ga ƴan ƙasa domin su yi amfani da ƴancin da kundin tsarin mulki ya ba su na yin zanga-zangar lumana."
"Duk wani yunƙuri na tauye waɗannan haƙƙoƙin ba kawai saɓawa kundin tsarin mulki bane, amma har da yin karan tsaye ga dimokuraɗiyyarmu."
- Atiku Abubakar
Gargaɗi kan zanga-zanga
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗi kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Kayode Egbetokun ya yi gargaɗi kan yin wani tashin hankali da fakewa da maimaita irin zanga-zangar da aka yi a ƙasar Kenya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng