Ana Harin Fara Zanga Zanga, Sufeto Janar na 'Yan Sanda Ya Aika da Sako Mai Zafi

Ana Harin Fara Zanga Zanga, Sufeto Janar na 'Yan Sanda Ya Aika da Sako Mai Zafi

  • Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗi kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ƙasar nan
  • Kayode Egbetokun ya yi gargaɗin cewa ƴan sanda ba za su zura ido ba su bari a fake da zanga-zangar domin tayar da rikici
  • Ya bayyana cewa sun mafiya yawa daga cikin masu shirya zanga-zangar ba su zaune a Najeriya amma suna so ne kawai su hargitsa ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sufeto-Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗi kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Kayode Egbetokun ya yi gargaɗi kan yin wani tashin hankali da fakewa da maimaita irin zanga-zangar da aka yi a ƙasar Kenya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga matasa masu shirin yin zanga zanga

Sufeto Janar na 'yan sanda ya yi gargadi
Kayode Egbetokun ya yi gargadi kan zanga-zanga Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sufeto-Janar na ƴan sandan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da manyan ƴan sanda na ƙasar nan a ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me shugaban ƴan sanda ya ce kan zanga-zanga?

Kayode Egbetokun ya shawarci masu shirya zanga-zangar da su dakatar da shirinsu domin ƴan sanda ba za su zura musu idanu ba suna kallo su tayar da hankula a ƙasar nan.

Shugaban ƴan sandan ya bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda abin da ya faru a lokacin zanga-zangar #EndSARS a faɗin ƙasar nan.

Babban jami'in ya ce har yanzu ƴan sanda ba su gama warkewa daga asarar da suka yi ba a lokacin.

Matsayar 'yan sanda kan zanga-zanga

"Matsayarmu ita ce zanga-zangar da ake shirin yi ba ta kamata kuma ya dace a fasa yin ta da gaggawa."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wanda ake zargi da 'kitsa' kisan janar na sojoji a Kano

"Muna da haƙƙin kare dukiyoyi da duk mutane masu bin doka da oda ba tare da la'akari da ƙabila, jinsi ko kalar fatarsu ba."
"Saboda haka ba zamu zauna mu zura idanu wasu baragurɓi su tayar da hankula ba ko sake lalata manyan kadarorin ƙasa masu muhimmanci."

- Kayode Egbetokun

Su waye ke shirya zanga-zanga?

A cewarsa ƴan sanda sun yi bincike kan mafi yawan masu shiryawa da ɗaukar nauyin zanga-zangar, kuma sun gano cewa da yawansu ba su zaune a cikin ƙasar nan, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

Ya ce ƴan sandan sun fahimci cewa mutanen suna so ne kawai su tayar da hargitsi a ƙasar nan da sunan zanga-zanga.

Tinubu ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi matasan ƴan Najeriya su hakura su janye shirinsu na yin zanga-zanga kan ƙuncin rayuwa a wata mai zuwa.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya za su shiga zanga zangar adawa da Tinubu? Miyetti Allah ta magantu

Shugaban ya kuma tabbatarwa da wadanda suka shirya zanga-zangar cewa ya ji kokensu kuma yana bakin kokarinsa wajen ganin an magance duk wata damuwa da ke damunsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng