Bayan Gyaran Kananan Hukumomi, Tinubu Ya Dauko Canza Fasalin Aikin Yan Sanda

Bayan Gyaran Kananan Hukumomi, Tinubu Ya Dauko Canza Fasalin Aikin Yan Sanda

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura takarda ga majalisar wakilai domin gyara kan dokokin yan sanda a Najeriya
  • Majalisar wakilai ta tabbatar da karbar takardar da shugaba Bola Tinubu ya turo mata da fara aiki a kanta da gaggawa
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Tinubu ya yi kokarin kwato hakkin kananan hukumomi daga wajen gwamnoni

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan kwato yancin kananan hukumomi, shugaba Bola Tinubu ya dauki hanyar gyara a aikin dan sanda.

A yanzu haka Bola Tinubu ya tura takarda ga majalisar tarayya domin yin gyara ga nadin shugaban yan sanda a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

Yan sanda
Tinubu zai yi gyara a aikin dan sanda. Hoto: Nigeria Police Force, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Majalisar wakilai ta wallafa a shafinta na Facebook cewa ta karbi takardar da shugaban kasar ya aike mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gyaran aikin dan sanda a Majalisa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci majalisar wakilai ta gyara dokar da take kayyade shekarun aikin sufeton yan sanda.

Dama dai idan sufeton yan sanda ya yi ritaya zai ajiye aiki amma dokar za ta ba shi damar cigaba da aiki har sai lokacin da shugaban kasa ya kayyade masa ya yi.

Ya ya dokar yan sanda za ta kasance?

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa a sabuwar dokar sufeton yan sanda zai rika yin shekaru hudu ne kan muƙami.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa sufeton yan sanda da yake kai, IGP Kayode Egbetokun ba lallai ya shiga cikin dokar ba.

Majalisa ta fara aiki kan dokar

Kara karanta wannan

A karon farko, Shugaba Tinubu ya yi magana kan matasa masu shirin yi masa zanga zanga

Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka majalisar wakilai ta yi karatu na biyu kan kudurin dokar aikin yan sandan.

Dadin dadawa, majalisar ta mika dokar ga kwamiti mai lura da aikin yan sanda domin yin nazari kan dokar.

Dele Momodu ya shawarci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu ya tura sako ga Bola Tinubu kan tafiyar da mulkin Najeriya.

Dele Momodu ya ce ya fahimci cewa duk ƙoƙarin da Bola Tinubu yake na raba tallafi na cikin neman samun mulki karo na biyu ne idan an tashi zabe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng