Hukumar EFCC ta yi Ram da Mai Dalilin Auren Bogi da Zargin Aikata Danyen Aiki

Hukumar EFCC ta yi Ram da Mai Dalilin Auren Bogi da Zargin Aikata Danyen Aiki

  • Hukumar hana yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta kama wani matashi da abokansa bisa laifin zamba
  • Haka kuma ana zargin matashi Audu Ishida da bude shafukan bogi da ke hada masoya inda ta nan ne ya ke cin kudin jama'a
  • Yanzu haka babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna na sauraron tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ta shigar gabanta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta bayyana cewa ta kama wani matashi mai dalilin aure na bogi.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta kama matashi, Audu Ishida da aka fi sani da Baddie Kylemili a bisa zargin damfara ta kafar intanet.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince 'danuwan Yahaya Bello da ake zargi da badakalar N3bn ya tafi kasar waje

Hukuma
Hukumar EFCC ta kama matashi mai dalilin aure Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Hukumar ta wallafa a shafinta na X cewa ana zargin matashin da yin sojan gona, samun kudin haramun da kuma halasta kudin haram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama matashin tare da wasu abokan huldarsa da su ka kware wajen damfara ta kafar intanet a Jos.

EFCC ta gurfanar da matashi kotu

Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce ta gurfanar da matashin da ake zargi da aika laifuffuka ta intanet gaban kotu, Jaridar Leadership ta wallafa.

Yanzu haka babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ce ke sauraron shari'ar matashi Audu Ishida karkashin jagorancin mai shari'a, Hauwa'u Buhari.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa an gano yadda Ishida ya bude shafukan sada zumunta da ke hada masoya, kuma ta nan ya ke damfarar jama'a.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Yan sanda sun dakume kwararren barawo ya na tsakiyar sata a Kaduna

An kuma bankado yadda ya rika samun kudi ta hanyar kafar inda ya ke musanya kyautar kudaden da ake ba shi zuwa Naira.

EFCC ta gurfanar da tsohon minista a kotu

A wani labarin kun ji cewa hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da tsohon ministan makamashi, Sale Mamman a gaban kotu bisa zargin badakala.

Hukumar EFCC na zargin Sale Mamman da hannu a cikin badakalar Naira Biliyan 33 na kudin kwangilar gina Mambila da Zungure, da sauran zarge-zarge da duka su ka kai 12.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.