Zanga Zanga: Tsohon Ministan Buhari Ya Fadawa Matasa Hadarin Hawa Tituna
- Tsohon Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari ya ba wa ma su shirin zanga-zanga shawarwari a kan illar yin haka ga zaman lafiya
- Sunday Dare, wanda shi ne tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa ya ce har yanzu jama'a ba su gama farfado wa daga zanga-zangar EndSARS ba
- Ya ce akwai fargabar bata-gari za su iya shiga rigar ma su zanga-zanga wajen kawo tashe-tashen hankula a kasa baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa a gwamnatin Buhari, Sunday Dare ya shawarci matasan kasar nan a kan hanyar samun saukin halin da ake ciki.
Tsohon Ministan ya ce akwai wata hanya da za a bi a maimakon a tafi zanga-zangar gama gari da aka shirya za a yi na kwanaki 15.
A wata hira da tsohon Ministan ya yi ta shafinsa na X, ya ce har yanzu jama'a na kokarin farfado wa daga cikin halin da zanga-zangar endSARS ya ya jefa 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akwai fargabar shiga bata-gari zanga-zanga
Tsohon Minista a gwamnatin Buhari, Sunday Dare ya gargadi matasa kan illar da zai iya biyon bayan zanga-zangar gama gari.
The Cable ta wallafa cewa Mista Dare ya ce akwai fargabar bata-gari za su iya shiga rigar masu zanga-zanga wajen tayar da hatsaniya a kasar nan.
Zanga-zanga: Tsohon Minista ya nemi a tattauna
Tsohon Ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare ya bayyana cewa kamata ya yi matasan kasar nan su zauna da gwamnati domin neman mafita.
Ya ce kamata ya yi a zauna, a tattauna da gwamnati a kan hanyar da ta fi dace wa wajen magance koken 'yan kasa.
Kungiya ta nemi tattaunawa maimakon zanga-zanga
A wani labarin kun ji yadda wata kungiyar Afrika ta ANPDD ta shawarci matasan Najeriya a kan bukatar su zauna a teburin tattauna wa da gwamnatin tarayya gabanin zanga-zanga.
Shugaban kungiyar, Prince Elias Odoemena ya ce gwamnati ta yi kokari wajen kawar da matsalolin kasar nan tun bayan tabbatar wa kananan hukumomi 'yancinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng