ANPPD: Kungiyar Afrika ta Fadawa Masu Shirya Zanga Zanga Abin da ya Kamata su yi

ANPPD: Kungiyar Afrika ta Fadawa Masu Shirya Zanga Zanga Abin da ya Kamata su yi

  • Wata kungiyar da ke rajin wanzar da zaman lafiya da ci gaba ta Afrika (ANPPD) ta bayar da shawarwari kan zanga-zangar gama gari da ake shirya gudanar wa
  • Kungiyar ta shawarci wadanda ke shirya zanga-zangar da su yi kokarin gana wa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima
  • Shugaban kungiyar, Prince Elias Odoemena ya ce ta hanyar tattauna wa za a samu abin da ake bukata maimakon zanga-zangar gama gari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Wata kungiyar rajin wanzar da zaman lafiya da ci gaba ta ANPPD ta shawarci masu shirin zanga-zanga da su dauki wani mataki na daban kafin daukar matakin.

Kara karanta wannan

"Kowa a fusace ya ke": NLC ta ba Tinubu mafita kan shirin zanga zanga

A ranar 1 Agusta, 2024 ne wasu fusatattun 'yan Najeriya su ka ce za su fito zanga-zangar nuna fushinsu kan halin matsin rayuwa da ake ciki.

Bola Tinubu
Kungiyar Afrika ta bayar da shawara ga masu shirya zanga-zanga Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kungiyar ta shawarci wadanda ke shirya zanga-zangar su nemi zama da shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zama da gwamnati zai kawo mafita," Kungiya

Shugaban kungiyar ANPPD, Prince Elias Odoemena ya bayyana cewa akwai bukatar a zauna da gwamnati a kan batun zanga-zangar.

Ya ce ko hukuncin kotu na baya-bayan nan zai kawo sauki a halin matsin da 'yan kasar nan ke ciki na kunci da wahala, Jaridar Blueprint ta wallafa.

Prince Odoemena ya kara da cewa ana zargin wasu gwamnoni da handame kudin kananan hukumomi wanda ya jawo matsaloli a yankunan.

Shugaban ya kara da cewa tabbatar wa kananan hukumomi 'yancin gashin kansu zai habaka ci gaba a kasar nan.

Kara karanta wannan

Sako zuwa ga Tinubu: NLC ta fadi hanyoyi 2 na hana matasan Najeriya yin zanga zanga

"Gwamnati ta zauna da matasa," NLC

A baya mun kawo labarin cewa kungiyar kwadago ta kasa, NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta zauna da masu shirin zanga-zangar gama gari domin samar da mafita.

Shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero ya ce doka ta ba wa 'yan kasa ikon gudanar da zanga-zanga, saboda haka zama a teburin sulhu ce hanyar da za a samu fahimtar juna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.