Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Kori Wasu Shugabanni Daga Aiki, Ya Ɗauko Gyara

Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Kori Wasu Shugabanni Daga Aiki, Ya Ɗauko Gyara

  • Gwamma Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da korar shugabannin rikon kwarya na kungiyar ƙwallon kafa ta jihar Kano watau Kano Pillars
  • Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano ya ce matakin da kwamishinan wasanni, Mustapha Kwankwaso ya ɗauka ya yi daidai
  • Shehu Wada Sagagi ya ce gwamnatin Kano ta fara ƙoƙarin sake fasalin Kano Pillas domin dawo da ƙungiyar kwallon kan ganiyarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan korar shugabannin rikon kwarya na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, Shehu Wada Sagagi ne ya tabbatar da hakan a wata hira da manema labarai a jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da korar shugabannin rikon kwarya a Kano Pillars Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A shekarun baya Kano Pillars na ɗaya daga cikin kungiyoyin da tauraruwarsu ke haskawa a gasar cin kofin firimiya na gida Najeriya, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya miƙa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi ga majalisa, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a baya-bayan nan ƙungiyar kwallon kafar ta jihar Kano ta samu koma baya, lamarin da ya kai ga sauye-sauyen masu horarwa.

Gwamna Abba ya tabbatar da matakin kwamishina

Da yake ƙarin haske kan korar shugabannin ƙungiyar kwallon na rikon kwarya, Shehu Sagagi ya ce kwamishinan matasa da wasanni Mustapha Kwankwaso ya yi daidai da ya sallame su.

Ya ce matakin da kwamishinan ya ɗauka bai saɓawa matsayar majalisar zartaswa ba kuma sai da ya nemi izinin Gwamma Abba Kabir gabanin korar ma'aikatan, New Telegraph ta rahoto.

Shehu ya ƙara da cewa tuni gwamnatin Kano ta fara kokarin sake fasalin ƙungiyar domin dawo da ita kan ganiyarta a harkokin kwallon ƙafa.

"Kwamishinan wasanni shi ne ke kula da Kano Pillars, ƙungiyar tana karkashin ma'aikatarsa, abin da ake so a koda yaushe ya rika taka-tsantsan.

Kara karanta wannan

Yusuf Gagdi: Abubuwan sani dangane da dan majalisar da ya siyawa 'yarsa motar kusan N100m

"Kwamishina bai aikata wani laifi ba, da izinin gwamnan ya ɗauki matakin, yanzu haka ya miƙa bukata ga mai girma gwamna yana jiran amincewarsa."

- Shehu Wada Sagagi.

Gwamna Abba ya ci gaba da rusau

A wani rahoton kuma, an ji 'yan kasuwa a jihar Kano da ke kan titin Jami'ar Bayero sun yi korafi kan kokarin ruguza musu wuraren sana'a.

Sai dai gwamnatin Kano ta hannun kwamishinan tsara birane ta bayyana cewa tana sane da abin da ke faruwa kuma haƙƙinta ne ta tabbatar da tsarin gine-gine.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262