Dubu Ta Cika: An Kama Wanda Ake Zargi da 'Kitsa' Kisan Janar Na Sojoji a Kano
- 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da tsara harin da aka kashe Birgediya Janar Udokwere Harrod mai ritaya a jihar Kano
- Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Bennett Igweh ya ce sun kama Hashiru Baku a Kano a lokacin da yake kokarin guduwa daga Najeriya
- A watan Yunin da ya gabata ne wasu ƴan fashi da makami suka shiga har gida suka kashe tsohon sojan tare da sace bindiga da wasu kayayyakinsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rundunar ƴan sanda reshen Abuja ta cafke Hashiru Baku, wanda ake zargin yana da hannu a tsara kisan Birgediya Janar Harold Udokwere.
Udokwere, Janar na rundunar sojojin Najeriya wanda ya yi ritaya ya rasa rayuwarsa ne lokacin da ƴan fashi suka kai farmaki gidansa ranar 22 ga watan Yuni, 2024.
Rahoton Leadership ya nuna cewa ƴan sanda sun cafke mutum huɗu da ake zargin suna da hannu a kisan a ranar 24 ga watan Yuni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun kama Hashiru a Kano
Da yake hira da ƴan jarida yayin nuna ƙarin wanda aka kama da zargin kitsa harin, kwamishinan ƴan sandan Abuja ya ce sun kama Hashiru Baku a jihar Kano.
CP Bennett Igweh ya ƙara da cewa wanda ake zargin na ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje, Premium Times ta ruwaito.
Kwamishinan ƴan sanda ya bayyana cewa jami'an ƴan sanda sun kama shi ne a loƙacin da yake ƙoƙarin guduwa daga ƙasar nan.
"A baya na nuna muku mutum hudu da suka je suka kashe Birgediya Janar Udokwere Harrod mai ritaya. A yau zan nuna maku wanda ya kitsa harin da kisan.
"Mun kwato bindigar marigayi janar, agogonsa da kuma sarƙar matarsa da suka sace a lokacin da suka shiga gidan. Wanda ya tsara kai harin nan mun kama shi.
"Yana tsare a gidan kaso lokacin da aka kai harin gidan yarin Kuje, ya samu dama ya tsere, maimakon ya tuba sai ya ƙara komawa ruwa. Mun kama shi a Kano yana koƙarin barin kasar nan."
- CO Bennett Igweh.
Dubun imfoma ta cika a Katsina
A wani rahoton kuma rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kara samun nasara a kan masu taimaka wa 'yan ta'adda da bayanan sirri domin kai hare-hare.
Daga cikin wadanda aka kama akwai yaro mai shekara 13, Umar Hassan da wani mai shekaru 70 Lawai Umaru da karin mutum biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng