Gwamna Dikko Radda Ya Kafa Tarihi, Ya Kirkiro Doka Kan Mata Masu Iddah a Katsina
- Gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Malam Dikko Radda ta kafa dokar bai wa matan da mazansu suka rasu hutun iddah
- Shugaban ma'aikatan jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ya ce tuni aka tura sanarwa ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati
- Addinin Musulunci ya tanadi lokacin iddah ga matan da Allah ya yiwa mazansu rasuwa inda suke shafe watanni huɗu da kwanaki 10
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bullo da dokar “hutun iddah”, domin bai wa mata ma’aikata damar zama a gida na tsawon watanni hudu da kwanaki goma.
A addinin Musulunci matan aure suna yin iddah tsawon watanni huɗu da kwanaki 10 idan Allah ya yiwa mazajensu rasuwa.
Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, Gwamnatin Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta kirkiro dokar Iddah ne domin bai wa mata hutun lokacin iddah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan kudirin da majalisar dokokin jihar ta amince da shi, wanda ya buƙaci ɓangaren zartarwa su duba yiwuwar bai wa ma'aikata mata hutun a lokacin da suke iddah.
Bayan gabatar da kudirin da shawarwari a gaban majalisar zartaswa ta jihar, ta amince da bai wa matan da mazajensu suka rasu hutu watanni huɗu da kwana 10.
Gwamnatin Katsina ta kafa dokar iddah
Shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Ya kara da cewa tuni aka tura takarda ga ma’aikatu da hukumomin jihar domin ba ma'aikata mata damar gudanar da iddah idan bukatar hakan ta taso, Punch ta rahoto.
"Mun gabatar da batun a gaban majalisar zartaswa domin shigar da dokar a cikin kundin dokokin aikin gwamnati, za a riƙa baiwa mata damar zama a gida su yi iddah idan sun rasa mazajensu.
"Yanzu haka mun tura sanarwa ga dukkan ma’aikatu da hukumomi domin ba wa ma'aikata mata hutun iddah. Yanzu ya zama doka,” inji shi.
Wata ma'aikaciyar lafiya a Katsina, Bilkisu Abdullahi ta nuna farin ciki da wannan doka yayin tattaunawa da wakilin mu.
Bilkisu ya shaidawa Legit Hausa cewa duk da mutuwa ba abim farin ciki ba ne amma yanzu macen da hakan ta faru da ita za ta yi iddah cikin kwanciyar hankali.
"Allah ya saka wa gwamna da alheri, wannan abu ne mai kyau domin ya kamata ko me za a yi a riƙa tunawa da mata. Allah ya taimaki gwamna mu kuma Allah ya bamu ikon sauke nauyin da ke kanmu," in ji ta.
Gwamna ya rungumi hukuncin kotun ƙoli
A wani rahoton na daban Malam Dikko Umaru Radda ya yi magana kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Gwamna Radda ya bayyana cewa dama tuni a jihar Katsina ƙananan hukumomi suka fara samun wani kaso na cin gashin kai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng