Ministar Tinubu Ta Fadi Dalilin da Ya Sanya Majalisa Ke Neman Hanata Rawar Gaban Hantsi
- Ministar harkokin mata ta yi zargin cewa akwai wasu shafaffu da mai a cikin gwamnati da ke neman hanata rawar gaban hantsi
- Uju Kennedy-Ohanenye ta ce an taso ta a gaba ne saboda ta ƙi ta sanya hannu kan wani bashin $500m da za a karɓo a hannun bankin duniya
- Zargin na ministar na zuwa ne bayan a kwanakin baya an titsiyeta a majalisar wakilai kan zargin karkatar da N1.5bn
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi zargin cewa akwai wasu shafaffu da mai a gwamnati da suka takura mata.
Ministar matar ta yi zargin cewa ana takura mata ne saboda ta ƙi sanya kan buƙatar karɓo bashin $500m daga bankin duniya.
Hakan na zuwa ne bayan a kwanakin baya kwamitin majalisar wakilai ya titsiyeta kan zargin karkatar da N1.5bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi ministar Tinubu ta yi?
Jaridar Thisday ta rahoto cewa ministar ta yi wannan zargin ne yayin wata hira ta wayar tarho da suka yi da ita.
"Akwai bashin $500m da ya kamata na sanyawa hannu, amma na ƙi sanyawa. Akwai kuma wani tun da farko na $100m."
"Dukkanin basussukan da suke karɓa ciki har da na bankin duniya da sauransu, ko kun san cewa ma'aikatan bankin duniyan a Najeriya suna karɓar kaso 40%?"
"Waɗannan mutanen ya kamata ku sanyawa ido. Ya kamata ku gano inda matsalar take sannan su barni na huta.
"Yanzu rayuwa ta na cikin hatsari saboda na ƙi sanya hannu kan bashin na $500m. Bari na gaya muku wani abu, idan na sanya hannu kan bashin nan zan samu kaso 5%, amma na ƙi sanyawa."
"Wannan na daga cikin dalilin da ya sanya majalisa da dukkaninsu suka taso ni a gaba."
- Uju Kennedy-Ohanenye
Matasa sun lalata allunan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa fusatattun matasa a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, sun lalata manyan allunan da aka kafa domin yi wa Shugaba Bola Tinubu maraba zuwa jihar.
A wani bidiyo da ya yaɗu, an nuna matasan suna hawa kan allunan dake ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu, mataimakinsa Shettima da Gwamna Mai Mala Buni suna yaga su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng