Gagarumar Zanga Zanga Ta Barke a Jihar Arewa, Bayanai Sun Fito
- Mazauna ƙaramar hukumar Kankara sun fito kan tituna domin nuna adawa da yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin
- Sun koka kan yadda ƴan bindigan suka addabi mutanen ƙauyukan yankin da hare-hare babu gaira babu dalili
- Sun dai gudanar da zanga-zangar ne a ranar Asabar, inda suka toshe manyan tituna tare da yin kira ga hukumomi su ɗauki matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Mazauna ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar.
Mutanen sun tare manyan tituna yayin da suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a ƙauyukan yankin.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu, cewar rahoton jaridar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun tare hanyar Marabar-Kankara zuwa Katsina da Kano da kuma hanyar da ta haɗa Malumfashi zuwa Funtua da jihar Kaduna.
Menene buƙatar masu zanga-zangar?
Ɗaya daga cikin mazauna yankin, Muhammad Sabiu, ya ce suna son gwamnati ta gaggauta magance matsalar saboda abin da ke faruwa a yankunan ya yi muni.
"A yanzu haka akwai gawarwakin mutanen da ƴan bindiga suka kashe a cikin daji, kuma sun hana mu kwashe su."
"Kisan ya faru ne kwanaki uku da suka gabata. Abin da ke faruwa dare da rana ke nan a cikin ƙauyukanmu."
"Muna kira ga gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen matsalar."
"Sun hana wasu daga cikinmu yin noma, domin haka rayuwa a waɗannan wuraren ta yi matukar wahala."
- Muhammad Sabiu
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Da aka tuntuɓi kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Nasiru Muazu-Danmusa, ya ce gwamnati na ƙoƙarin magance matsalolin da masu zanga-zangar suka koka a kai.
"Zanga-zangar ta ƙare, kuma tuni Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi ya yiwa masu zanga-zangar jawabi."
Ƴan sanda sun cafke miyagu a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar damƙe wasu mutane hudu da ke tattara bayanan sirrin jama'a su na miƙawa masu garkuwa da mutane.
Wani yaro mai shekaru 13, Umar Hassan na daga cikin mutane hudu da jami'an tsaron su ka cafke bisa zargin taimaka wa miyagun.
Asali: Legit.ng