Malamin Addini Ya Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Jefa 'Yan Najeriya Cikin Wuya, Ya Ba Shi Mafita
- Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi magana kan haƙin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki a mulkin Shugaba Bola Tinubu
- Shugaban na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Tinubu ne suka jefa ƙasar nan cikin halin wuya
- Ya nuna cewa gwamnatin ba ta ɗaukar shawara ko kaɗan kuma idan ba a yi taka tsan-tsan ba akwai wahala na nan tafe a nan gaba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Malamin addinin ya bayyana cewa manufofin tattalin arziƙi na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun yi tsauri kuma sun ƙara rura wutar wahalar da ake sha a ƙasa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a wajen ƙaddamar da littafinsa mai suna 'Warnings to The Nations', cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Primate Ayodele ya caccaki Tinubu
Primate Ayodele ya bayyana cewa da gwamnati mai ci na ɗaukar shawara da ta yiwa saura zarra, amma manufofin da ta zo da su ba su amfani ƴan ƙasar nan ba.
Malamin addinin ya bayyana cewa matakan da gwamnatin Tinubu ta ɗauka sun lalata ƙasar nan, sannan idan ba a yi taka tsan-tsan ba mutane za su ci gaba shiga cikin halin wuya da ƙunci, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.
"Da gwamnatin Tinubu na ɗaukar shawara da ta yiwa saura zarra. Gwamnatin na kawo manufofi marasa kyau saboda ba su ake buƙata ba."
"Raba kuɗi da shinkafa ga mutane zai ƙara lalata tattatin arziƙi ne kawai."
"Tsarin harajin bai taimakawa ƙasar nan. Akwai kura-kurai da dama a gwamnatin da har yanzu an kasa yin magana a kansu. Sannan idan ba a yi taka tsan-tsan ba, haka za su lalata ƙasar nan mutane su ƙara shan wuya da ƙunci."
- Primate Babatunde Ayodele
Malamin addini ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Adam Muhammad Albaniy ya magantu kan halin kunci da ake ciki.
Malamin ya ce hanya daya ce ta dakile halin kunci da ake ciki shi ne dawo da tallafin mai ba wai raba shinkafa ba.
Asali: Legit.ng