Gwamnan Arewa Ya Shirya Kawo Karshen Matsalar Wutar Lantarki a Jiharsa
- Gwamnatin jihar Katsina ta fara ƙoƙarin ganin ta kawo ƙarshen matsalar ɗaukewar wutar lantarki
- Gwamnatin ta shirya yin haɗaka da kamfanonin ƙasashen waje da na cikin gida domin samar da tashar wutar lantarki a jihar
- Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara na jihar ne ya bayyana hakan inda ya yi ƙarin haske kan wannan shirin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta shirya samar da tashar wutar lantarki domin amfanin gidaje da masana'antu.
Gwamnatin ta shirya yin haɗaka da kamfanonin ƙasashen waje da na cikin gida domin cimma wannan manufar.
Shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara ta jihar, Alhaji Abdullahi Matazu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Katsina, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Katsina za ta kafa tashar lantarki
Ya bayyana cewa, da zarar an kafa tashar wutar lantarki za ta samar da wutar lantarki domin tabbatar da samar da wutar lantarki akai-akai domin amfanin gidaje masana'antu.
Alhaji Abdullahi Matazu, ya faɗi hakan ne yayin da yake sanya ido kan yadda ake ci gaba da girka na’urar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a gidan gwamnati da ke Katsina.
Ya ƙara da cewa aikin samar da wutar lantarkin mai amfani da hasken rana wani mataki ne da gwamnatin Radda ta ɗauka domin magance matsalar ɗauke wutar lantarki da kuma rage kuɗin da ake kashewa wajen siyan man dizal.
"Ɗaukewar wutar lantarki na kawo cikas wajen gudanar da ayyuka musamman a manyan asibitoci, wanda hakan ya sanya gwamnati ta koma amfani da hasken rana domin samar da lantarki ta yadda marasa lafiya za su samu kulawa."
"Shirin samar da wutar lantarkin ta hanyar amfani da hasken rana idan aka kammala, zai amfani dukkanin manyan asibitocin jihar, daga nan sai makarantun gwamnati su biyu baya."
- Alhaji Abdullahi Matazu
Batun ƴancin ƙananan hukumomi a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ce zai aiwatar da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Kotun Ƙolin dai ta ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu biyo bayan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnoni.
Asali: Legit.ng