Dangote Ya Musanta Zargin Samar da Dizal Mara Inganci, Ya Kalubalanci Hukumar NMDPRA
- Aliko Dangote ya yi martani kan zargin cewa matatar man fetur ɗinsa na samar da man dizal mara inganci
- Shugaban na rukunonin kamfanin Dangote ya bayyana cewa man dizal ɗin da matatar ke samarwa ya fi wanda ake shigo da shi daga ƙasar waje
- Martanin Dangote na zuwa ne bayan shugaban hukumar NMDPRA ya yi iƙirarin cewa man dizal ɗin na Dangote bai kai ingancin wanda ke shigo da shi daga waje ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya musanta cewa zargin cewa man dizal da matatar man fetur ɗinsa ke samarwa ba ya da inganci.
Dangote ya tabbatar da cewa kayayyakin da aka tace a matatar man fetur ɗinsa, suna da inganci idan aka kwatanta da na waje da aka shigo da su kuma sun cika ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.
Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa ne bayan da shugabannin majalisar wakilai da suka ziyarci matatar man fetur ɗin suka gwada man dizal da aka siyo a waje tare da na Dangote a ɗakin gwaje-gwaje na zamani, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwajin da aka yi ya nuna cewa man dizal na Dangote yana da sinadarin sulfur na 87.6ppm yayin da sauran samfuran biyu suke ɗauke da sinadarin sulfur da ya wuce 1800ppm da 2000ppm, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Dangote ya ƙalubalanci NMDPRA
Dangote ya jaddada cewa, gwajin ya ƙaryata iƙirarin shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, wanda ya ce cewa dizal ɗin da ake shigowa da shi ya fi wanda ake samarwa a cikin Najeriya inganci.
Dangote ya fito ƙarara ya ƙalubalanci hukumar da ta kwatanta ingancin kayayyakin da aka tace daga matatarsa da waɗanda ake shigo da su daga ƙasashen waje.
"Muna samar da dizal mafi inganci a Najeriya. Akwai ban takaici cewa maimakon kare kasuwar, hukumar na ƙoƙarin lalata ta."
"Ƙofofin mu a buɗe suke ga hukumar domin ta zo ta yi gwaje-gwaje kan kayayyakin mu a kowane lokaci, gaskiya na da muhimmanci a wajenmu."
"Yana da kyau hukumar ta nuna ɗakin gwaje-gwajenta ta yadda ƴan Najeriya za su yi alƙalanci."
- Aliko Dangote
Dangote na zama a gidan haya
A wani labarin kuma, kun ji cewa attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ba shi da gida a birnin Landan ko a ƙasar Amurka.
Dangote ya kuma bayyana cewa gidan da yake zaune a duk lokacin da yaje babban birnin tarayya Abuja, ba nasa ba ne.
Asali: Legit.ng