Zanga Zangar Adawa da Tinubu Ta Samu Cikas Bayan Wasu Matasan Arewa Sun Fice

Zanga Zangar Adawa da Tinubu Ta Samu Cikas Bayan Wasu Matasan Arewa Sun Fice

  • Wasu matasan yankin Arewa ta Tsakiya a ƙarƙashin gamayyar ƙungiyar NCYG, sun nesanta kansu daga zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan
  • Matasan sun bayyana cewa a cikin shekara ɗaya, Shugaba Bola Tinubu ya samu nasarori masu yawa
  • Sun yi kira ga matasa da su kasance masu haƙuri da nuna goyon baya ga gwamnati maimakon su bari wasu ƴan siyasa su yi amfani da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Wasu matasa daga yankin Arewa ta Tsakiya sun nesanta kansu daga zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Umar Bago na jihar Neja.

Matasan a ƙarƙashin gamayyar ƙungiyoyin matasan yankin Arewa ta tsakiya (NCYG) da suka haɗa da matasan yankin tsakiyar Najeriya, sune suka bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa ƴan ƙwadago alƙawari 1 bayan amincewa da albashin N70,000 a Aso Villa

Matasan Arewa ta Tsakiya sun fasa zanga-zanga
Kungiyar NCYG ta fasa shiga zanga-zanga Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Abdullahi Mohammed da Fidelis Elaigwu suka sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yabawa Tinubu da Gwamna Bago

Ƙungiyar ta cimma wannan matsayar ne bayan tantance ayyukan da shugabannin biyu suka yi.

Sun bayyana cewa ayyukan shugabannin sun kawo fata, damarmaki, da murmushi a fuskokin ƴan Najeriya, musamman al’ummar yankin Arewa ta tsakiya.

Ƙungiyar ta bayyana gwamnatin Shugaba Tinubu a matsayin wata fitila mai haske wacce a cikin shekara guda kacal ta haskaka hanyar samun kyakkyawar makoma ga Najeriya.

Sun ce Gwamna Bago ya samu ci gaba sosai a gwamnatinsa wajen mayar da hankali kan noma, ilimi, da samar da sana'o'i ga matasa.

Wace shawara suka ba matasa kan zanga-zanga?

"Mun fahimci cewa har yanzu akwai ƙalubale, amma mun yi imanin cewa Shugaba Tinubu da Gwamna Bago suna aiki tuƙuru domin magance su."

Kara karanta wannan

UTME: Jerin sunaye da jihohin ɗaliban da suka yiwa jarabawar JAMB cin kaca a 2024

"Muna kira ga ƴan uwanmu matasa da su kasance masu haƙuri, ba da goyon baya, da kuma kyautata zaman rayuwarsu, maimakon su bari ƴan siyasa su yi amfani da su."

"Mu haɗa kai domin gina kyakkyawar makoma ga kanmu, yankinmu, da ƙasarmu."

- Ƙungiyar NCYG

Gwamna Bago ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Gwamna Bago ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa matasan jihar Neja ba za su shiga zanga-zangar ba wacce za a yi a faɗin ƙasar nan daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng