Hadimin Tinubu Ya Fallasa Sunayen Masu Shirya Zanga Zangar Adawa da Gwamnati
- Hadimin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai ya yi zargin cewa magoya bayan Peter Obi ne ke shirya zanga-zangar da ake shirin yi
- Bayo Onanuga ya bayyana cewa ya kamata a ɗora alhakin duk abin da ya biyo bayan zanga-zangar a kan ɗan takarar shugaban ƙasan na jam'iyyar LP
- Zargin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta shirye-shirye kan gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hadimin shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya caccaki magoya bayan Peter Obi kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.
Bayo Onanuga ya bayyana cewa magoya bayan Peter Obi ne ke shirya zanga-zangar da ake yi shirin yi a ranar 1 ga watan Agustan 2024.
Onanuga ya bayyana cewa magoya bayan Peter Obi ne ke shirin tayar da rikici a ƙasar nan, saboda haka dole ne a ɗora alhaki a kansa kan duk abin da ya biyo bayan zanga-zangar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi hadimin Tinubu ya yi?
Hadimin na Shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai ya bayyana hakan ne a wani dogon rubutu da ya yi a shafinsa na X ranar Asabar, 20 ga watan Yulin 2024.
Onanuga ya yi iƙirarin cewa masu shirya zanga-zangar ƙin jinin gwamnati su ne waɗanda suka kutsa cikin zanga-zangar #EndSARS a shekarar 2020 domin haifar da tarzoma a faɗin ƙasar nan.
"Kada a yaudare ku: Ƴan tawayen da ke shirin gudanar da zanga-zangar a fadin ƙasar nan, magoya bayan Peter Obi ne, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour. Kuma ya kamata a ɗora masa alhakin duk wani rikici da ya taso bayan zanga-zangar."
"Masu shirya zanga-zangar dai su ne mutanen da shugaban IPOB Nnamdi Kanu ya ingiza suka ƙaddamar da zanga-zangar barna ta ENDSARS a Najeriya a watan Oktoban 2020."
"Shekara biyu bayan ENDSARS, IPOB da waɗanda aka hurewa kunne sun shiga jam'iyyar LP a 2022 domin marawa Peter Obi baya, mai goyon bayan manufarsu."
"Su ne mutanen da ke yaɗa kalaman ‘EndBadGovernance’, ‘Tinubu Must Go,’ da ‘Revolution2024’. Su ba masu son dimokuradiyya ba ne, ƴan a fasa kowa ya rasa ne."
- Bayo Onanuga
Karanta wasu labaran kan zanga-zanga
- Zanga-zanga ta samu babban koma baya, an saka sabanin kabilanci a cikin tafiyar
- Adawa da Tinubu: Gwamnati ta gano wadanda ne daukar nauyin matasa su yi zanga-zanga
- Tarihi bai manta ba: Nasarori da matsalolin da aka samu a lokutan zanga-zanga a baya a Najeriya
Matasan Neja ba za su zanga-zanga ba
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Gwamna Bago ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa matasan jihar Neja ba za su shiga zanga-zangar ba wacce za a yi a faɗin ƙasar nan daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng