Shugabannin Majalisar Wakilai Sun Kai Ziyara Matatar Ɗangote, Bayanai Sun Fito

Shugabannin Majalisar Wakilai Sun Kai Ziyara Matatar Ɗangote, Bayanai Sun Fito

  • Jagororin majalisar wakilai karkashin Rt. Hon Tajudeen Abbas sun kai ziyara matatar Ɗangote da ke yankin Lekki a jihar Legas yau Asabar
  • Ƴan majalisar sun kai wannan ziyara ne domin duba yadda aikin matatar ke tafiya yayin da take shirin fara sayar da man fetur a watan Agusta
  • Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote tare da tawagarsa ne suka tarbi ƴan majalisar a jihar Legas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Tawagar majalisar wakilan tarayya ta ziyarci katafariyar matatar man hamshakin ɗan kasuwar nan Alhaji Aliko Ɗangote da ke jihar Legas.

Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas shi ne ya jagoranci tawagar ƴan majalisar zuwa matatar Ɗangote da ke Lekki Free Trade Zone a Legas.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun kashe basarake mai martaba da ɗansa a Arewa

Matatar Dangote.
Jagororin majalisar wakilai ta ƙasa sun ziyarci matatar Ɗangote Hoto
Asali: Getty Images

Ƴan majalisar sun isa matatar da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Asabar, 20 ga watan Yuli, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar Tajudeen Abbas ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Yadda Ɗangote ya tarbi ƴan majalisa

Attajirin da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote da jagororin matatar ne suka tarbi ‘yan majalisar.

Ana sa ran ƴan majalisar za su zagaya su duba yanayin aikin matatar mai ƙarfin ta ce gangar mai 650,000 yayin wannan ziayara.

Wannan ziyara ta zama ta biyu da ‘yan majalisar tarayya suka kai matatar man cikin watanni biyu da suka shige.

Haka zalika ziyarar ta zo a daidai lokaci mai muhimmanci wanda matatar man ke shirin fara bayar da man fetur a watan Agusta mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu zai shilla zuwa kasar waje ana shirin fara zanga zanga

A watan Yuni, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jagoranci tawagar sanaroci zuwa matatar man domin duba yadda aiki ke tafiya.

Sanata Akpabio ya yaba da aikin tare da yin alkawarin cewa majalisar dattawa za ta yi ƙoƙarin tallafawa matatar.

Ɗangote ya shirya farfaɗo da tattalin arziki

A wani rahoton Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa tattalina arzikin kasar nan zai farfado nan da watanni kadan

Ya bayyana haka ne jim kadan bayan shugaban kasa, Bola Tinubu ya rantsar da shi da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren kasuwanci

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262