'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Kashe Basarake Mai Martaba da Ɗansa a Arewa

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Kashe Basarake Mai Martaba da Ɗansa a Arewa

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki kan titin Takum zuwa Chanchangi, sun halaka basarake da ɗansa ranar Jumu'a da yamma a jihar Taraba
  • Gwamna Agbu Kefas ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa
  • Kefas ya bayyana cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba har sai an kama maharan da suka kashe basaraken domin su girbi abin da suka shuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Wasu ƴan bindiga sun hallaka basaraken kauyen Chanchangi da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba, Kumbiya Tanimu da ɗansa mai suna Yusuf.

Maharan sun yi kwantan ɓauna tare ɗa hallaka basaraken da ɗansa a kan titin Takum-Chanchangi a lokacin da suke hanyar dawowa daga jana'iza a Takum ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Satar Akuya ta jawo matar aure ta buga wa mijinta gatari, ya mutu nan take

Gwamna Agbu Kefas na Taraba.
Yan bindiga sun yi ajalin basarake da ɗansa a jihar Taraba Hoto: Agbu Kefas
Asali: Facebook

Gwamna Agbu Kefas ya ɗauki mataki

Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya umarci jami’an tsaro da kamo makasan tare da gurfanar da su gaban kuliya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Emmanuel Bello ya fitar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Kefas ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin, al'ummar Chanchangi da daukacin mutanen ƙaramar hukumar Takum bisa wannan rashi.

"Gwamna ya roƙi jama’ar garin Takum su kwantar da hankalinsu, ya ce ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen kama maharan da gurfanar da su gaban kuliya cikin kankanin lokaci,” in ji Mista Bello.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar raya yankin, James Baka ya fitar, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su kamo wadanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya tsokano rigima, ya faɗi gwamnan PDP da ya yi yunƙurin kashe shi

Wannan dai shi ne karo na uku a bana da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kashe basaraken gargajiya a jihar Taraba, cewar Channels tv.

An kashe dagaci a Kaduna

Kuna da labarin Ƴan bindiga sun je har gida sun kashe dagacin kauyen Kurmin-Kare da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Wani mazanin kauyen, Shehu Baba ya bayyana cewa bayan kashe basaraken, ƴan bindigar sun yi awon gaba da mutum uku a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262