Sanata Ali Ndume Ya Tura Sako Mai Zafi Ga Tinubu Bayan Cire Shi Daga Mukaminsa

Sanata Ali Ndume Ya Tura Sako Mai Zafi Ga Tinubu Bayan Cire Shi Daga Mukaminsa

  • Tsohon babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa ya ce bai yi laifi ba domin ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yana kan bakansa bisa sukar shugaban ƙasan da ya yi kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasa
  • Ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya saurari koken ƴan Najeriya da kunnen basira domin suna cikin mawuyacin hali

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Sanata Ali Ndume, ya ce ko kaɗan bai yi laifi ba kan sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ndume ya kuma ce babu wani dalili da zai sanya ya ba da haƙuri duk da tsige shi da aka yi daga kan muƙamin babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani ga Ganduje, ya faɗi yadda Buhari da Tinubu suka jawo shi APC

Ndume ya ba Tinubu shawara
Sanata Ali Ndume ya ba Shugaba Tinubu shawara Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen. Mohammed Ali Ndume
Asali: Facebook

Sanata Ali Ndume wanda yake wakiltar Borno ta Kudu ya yi martani kan tsige shi inda ya ce yana kan bakansa bisa abubuwan da ya ce kan gwamnatin Tinubu da suka jawo ya rasa muƙaminsa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Ndume ya ba Tinubu?

Yayin da yake bayyana matakin da ya ɗauka a matsayin mai kishin ƙasa, Ndume ya shawarci Shugaba Tinubu da ya saurari kukan ƴan Najeriya kuma ya gaggauta magance matsalolin suke ciki, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

"Ina nan kan baka na cewa rashin kishin ƙasa ne a riƙa goyon bayan shugaban ƙasa kan duk abin da ya yi. Kishin ƙasa ne faɗar gaskiya ba ga shugaban ƙasa kaɗai ba amma har ga kowa."
"Rashin kishin ƙasa ne a ƙi gayawa masu mulki gaski gaskiya ko wani daban kuma ina nan a kan wannan matsayin. Ta hanyar yin hakan, na san cewa Allah yana tare da duk mai faɗin gaskiya."

Kara karanta wannan

Ali Ndume ya bayyana matsayarsa kan sabon mukamin da aka ba shi a majalisa

"Saboda haka na san cewa ban yi kuskure ba. Kuma ina roƙon shugaban ƙasa, wanda a yanzu ina sa ran cewa saƙon ya isa gare shi, ya duba abin da na faɗa, ya ɗauki matakan da suka dace domin kawar da wahalar da mutane ke sha."

- Sanata Ali Ndume

Ya ce ya ji daɗi cewa NLC da Tinubu sun amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi amma ya yi kaɗan, inda ya ƙara kira ga shugaban ƙasan da ya saurari buƙatun ƴan Najeriya da kunnen basira.

Ndume ya ƙi karɓar sabon muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume, ya yi watsi da naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yawon buɗe ido.

Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya ba Ali Ndume sabon muƙamin biyo bayan tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa na majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng