Ali Ndume Ya Bayyana Matsayarsa Kan Sabon Mukamin da Aka Ba Shi a Majalisa
- Tsohon babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ki karɓar sabon naɗin da aka yi masa a majalisa
- Sanatan ya ƙi karɓar sabon muƙamin da shugaban majalisar ya ba shi na shugaban kwamitin harkokin yawon buɗe ido
- Sanatan na Borno ta Kudu ya bayyana cewa bai yi nadamar kalaman da ya yi ba kan halin da ake ciki a ƙasar nan, wanda hakan ya sanya ya rasa muƙaminsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sanata Ali Ndume, ya yi watsi da naɗin da aka yi masa a matsayin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin yawon buɗe ido.
Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ne ya ba Ali Ndume sabon muƙamin biyo bayan tsige shi daga muƙamin mai tsawatarwa na majalisar.
Ndume ya yi martani kan rasa muƙaminsa
Sanata Ali Ndume yayin da yake mayar da martani game da tsige shi da aka yi daga muƙaminsa, ya ce ko kaɗan bai yi naɗama ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Sanatan ya bayyana cewa yana nan kan bakansa kan kalaman da ya yi dangane da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasa.
'Dan majalisar ya ƙara da cewa ƴan Najeriya na cikin yunwa kuma a fusace suke, rahoton The Punch ta tabbatar da labarin nan.
Ya ƙara da cewa Allah yana tare da mai gaskiya kuma rashin kishin ƙasa ne a gayawa shugabanni gaskiya.
Meyasa Ndume ya ƙi karɓar sabon muƙamin?
"Dangane da cire ni daga muƙami na, ban damu da hakan ba. Roƙo na aka yi na karɓi muƙamin babban mai tsawatarwa saboda sanin cewa na jagoranci yaƙin neman zaɓen Akpabio a matsayin shugaban majalisa."
"Roƙo na aka yi na zaɓi kwamitin da na ke so sannan sai na zaɓi mataimakin shugaban kwamitin kasafin kuɗi. Ban damu ba ko kaɗan."
"Na fahimci cewa an bani shugaban kwamitin harkokin yawon buɗe ido, babu wanda ya sanar da ni, amma ina so na bayyana a nan cewa na ƙi amincewa da wannan muƙamin saboda dalilai biyu."
"Ni ba mai yawon buɗe ido ba ne kuma ba na sha'awar zama shugaban kwamitin yawon buɗe ido. Ba ni da masaniya sosai a kan harkokin yawon buɗe ido."
- Sanata Ali Ndume
Atiku ya caccaki tsige Ali Ndume
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya caccaki majalisa kan yadda ta tsige bulaliyarta, Sanata Ali Ndume saboda sukar shugaban ƙasa.
Atiku Abubakar wanda ya nuna takaicinsa kan yadda ƴan majalisar suka zama marasa ra'ayin kansu ya ce lokaci ya yi da za su takawa ɗabi'unsu birki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng