Surukin Ganduje, Ɗan Tsohon Gwamna da Wasu Mutane da Tinubu Ya Ba Muƙamai a Mako 1
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - A makon jiya tsakanin 8 zuwa 14 ga watan Yuli, Bola Ahmed Tinubu ya yi naɗe-naɗe da dama a hukumomi da majalisun gudanarwa na hukumomin tarayya.
Daga cikin waɗanda mai girma shugaban ƙasa ya bai wa mukami a makon har da ƴaƴan tsofaffin gwamnoni, sanata da tsohon shugaban hukumar zaɓe INEC.
Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen waɗanda Tinubu ya naɗa a makon da ya wuce tare da muƙaman da ya ba su. Ga su kamar haka
1. Farfesa Attahiru Jega
Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban kwamitin aiwatar da garambawul kan harkokin kiwon dabbobi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya sanar da naɗin Jega ne a wurin taron kaddamar da kwamitin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Talata, 9 ga Yuli.
2. Naɗin shugaban NPA
A wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya wallafa a Facebook, Bola Tinubu ya sauke Mohammed Bello-Koko daga matsayin shugaban hukumar kula da tashoshin ruwa (NPA)
Tinubu ya kuma maye gurbinsa da Abubakar Dantsoho wanda zai shafe shekaru biyar yana jagorantar NPA bayan naɗinsa a ranar 12 ga watan Yuli.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya naɗa Bello-Koko a matsayin mukaddashin daraktan hukumar a watan Mayun 2021.
3. Tsohon sanatan Kano
A ranar Asabar, 13 ga watan Yuli, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon sanatan Kano ta Tsakiya, Bashir Lado Mohammed a matsayin mai taimaka masa kan harkokin majalisar dattawa.
Sanata Lado sanannen ɗan siyasa ne a Kano kuma ɗan kasuwa, ya taɓa rike shugaban hukumar yaƙi da safarar mutane NAPTIP.
4. Baffa Ɗanagundi
Har ila yau, Tinubu bai bar Kano ba, ya naɗa Baffa Ɗanagundi a matsayin sabon shugaban hukumar kula da inganci da kuma nagartar ayyuka.
Baffa Ɗanagundi fitaccen ɗan siyasa ne a Kano kuma ya rike shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar.
5. PenCom da NSITF
Hukumar Fansho ta Kasa (PenCom) hukumar inshora ta NSITF sun yi sababbin jagorori a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban Ƙasa Tinubu ya naɗa Omolola Oloworaran a matsayin babban daraktan Pencom da Oluwaseun Faleye a matsayin manajan darakta a hukumar NSITF.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
6. Surukin Ganduje kuma ɗan tsohon gwamna
Bola Tinubu ya sanar da naɗin Idris Ajimobi, ɗan marigayi tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi a matsayin hadiminsa na ɓangaren kula da kiwon dabbobi.
Idris Ajimobi ya kasance surukin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje wanda ke auren ƴarsa mai suna Fatima.
7. Tinubu ya ƙara naɗa ɗan tsohon gwamna
Duk dai a ranar Asabar, Bola Tinubu ya amince da nadin dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo a matsayin shugaban hukumar NALDA.
Ya buƙaci Adebayo ya yi amfani da gogewarsa wajen kawo ci gaba a NALDA, hukumar da ke kula da ci gaban harkokin noma a Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook.
8. Tinubu ya naɗa shugabannin hukumomi 6
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar da jerin sunayen sababbin shugabannin hukumomi da Bola Tinubu ya naɗa duk a ranar Asabar.
a. Mainasara Umar Kogo - Hukumar ɗa'ar ma'ikata (CCT)
b. Umar Ibrahim Mohammed - Hukumar NIHSA
c. Mista Silas Agara - NDE
d. Tosin Adeyanju - Hukumar NLTF
e. Saleh Abubakar - Hukumar NAGGW
f. Oluwaseun Faleye - hukumar NSITF.
Tinubu ya ba jihohi tirelolin shinkafa
A wani rahoton kuma yayin da ake fama da yunwa, Gwamnatin Tarayya ta bayar da gudummuwar tirelolin shinkafa ga jihohi 36 da birnin tarayya Abuja.
Ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya ce an bada wannan tallafin ne domin rabawa ƴan Najeriya masu karamin karfi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng