'Yan Ta’adda Sun Farmaki Tawagar Mataimakin Gwamna Awanni Bayan Kotu Ta Maida Shi Kan Mulki

'Yan Ta’adda Sun Farmaki Tawagar Mataimakin Gwamna Awanni Bayan Kotu Ta Maida Shi Kan Mulki

  • Philip Shaibu, wanda kotu ta mayar kan kujerar mataimakin gwamnan Edo ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa a Benin
  • An ce an kai wa Philip Shaibu wanda yake tare da dan takarar gwamnan APC a zaben jihar na watan Satumba harin ne a ranar Alhamis
  • Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an kashe dogarin mataimakin gwamnan yayin da wasu jami'an tsaro suka samu raunuka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kashe wani dan sanda mai suna Sifeta Onu Ako yayin wata liyafar dawowar mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya tsallake rijiya da baya, iyalansa 3 sun mutu a gobara

Dan sandan ya kasance dogari ne ga dan takarar APC, Monday Okpebolo, a zaben gwamna da za a yi a ranar 21 ga Satumba, 2024 a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya fuskanci harin kisa a Benin, a ranar Alhamis.
Philip Shaibu ya tsira daga harin kisan gilla a Benin. Hoto: @HonPhilipShaibu
Asali: Twitter

Kakakin ‘yan sanda a jihar, Chidi Nwabuzor, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a kan hanyar tashar jirgin sama ta jihar inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamna ya sha da kyar

'Yan bindiga sun farmaki tawagar Kwamared Philip Shaibu, mataimakin gwamnan Edo da aka tsige amma kotu ta mayar da shi, a wani yunkuri na hallaka shi.

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke tsige Shaibu, inda shi kuma ya koma Edo daga Abuja a lokacin da aka kai wa ayarin motocinsa harin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar da ke cikin wata mota a kofar fita daga filin jirgin, sun bude wa ayarin motocin wuta, lamarin da ya kai ga musayar wuta da jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mata 5 sun tsere daga hannun 'yan bindiga, an yi jana'izar wasu mutum 5

Zamfara: Mata 5 da aka sace sun kubuto

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla mata biyar ciki har da mai shayarwa daga cikin akalla mutane 100 da 'yan bindiga suka sace a kauyen Dan Isa a jihar Zamfara sun kubuto.

An ce sun tsero ne daga hannun 'yan bindigar yayin da suke kan hanyar kaisu inda za a ajiye su, kamar yadda Malama Na'imah ta ba da labari bayan dawowarta gida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.