Bayan Rage Albashi 'Yan Majalisa Sun Nemi Muhimmiyar Bukata Wajen 'Yan Najeriya

Bayan Rage Albashi 'Yan Majalisa Sun Nemi Muhimmiyar Bukata Wajen 'Yan Najeriya

  • Majalisar wakilai ta yi magana kan shirye-shiryen da ake yi na gudanar da zanga-zanga kan halin ƙuncin da ake ciki a faɗin ƙasar nan
  • Ƴan majalisar sun buƙaci masu shirya zanga-zangar da su haƙura su fara gudanar da ita tare da rungumar tattaunawa da gwamnati domin samun mafita
  • Sun yi nuni da cewa ba a Najeriya ba ne kaɗai ake fuskantar ƙalubale, sannan shekara ɗaya ta mulkin Shugaba Bola Tinubu ta yi kaɗan ta gyara matsalolin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta buƙaci masu shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan da su haƙura.

Majalisar ta yi wannan kiran ne a ranar Alhamis inda ta buƙaci masu shirya zanga-zangar ɗauki dangana tare da tattaunawa da gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gano abin da ya ta'azzara matsalar rashin tsaro

'Yan majalisa sun bukaci 'yan Najeriya kada su yi zanga-zanga
'Yan majalisa ba su son a yi zanga-zanga Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan wani ƙudiri mai muhimmanci da Honarabul Ibrahim Isiaka, ya gabatar a gaban majalisar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisa sun ba ƴan Najeriya shawara

Ƴan majalisar sun amince da cewa ƙalubalen da ake fuskanta ba a Najeriya ba ne kaɗai, inda suka yi nuni da cewa sai an sha wuya ake samun canjin da ake buƙata.

Sun yi kira ga ƴan Najeriya da ka da su manta da irin sauye-sauye da nasarorin da gwamnati mai ci ta samu domin ci gaban ƙasar nan.

Da yake na sa jawabin, mataimakin kakakin majalisar wakilan, Benjamin Kalu, ya goyi bayan kuɗirin da aka gabatar.

"A ƙarawa Tinubu lokaci": Hon. Ben Kalu

Benjamin Kalu ya bayyana cewa shekara ɗaya ta mulkin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi kaɗan wajen magance matsalolin da ke addabar ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fice daga shiga zanga zanga kan gwamnatin Tinubu, sun bayyana dalili

Ya kuma gabatar da ƙudiri a gaban majalisar domin rage kaso 50% na albashinsu zuwa nan da watanni domin a tallafawa ƴan Najeriya.

Benjamin Kalu ya bayyana cewa ƴan majalisar na karɓar N600,000 duk wata a matsayin albashi.

Zulum ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babagana Umara Zulum ya ba al'ummar Borno da ƴan Najeriya baki ɗaya shawara kan zanga-zangar da ake shirin yi.

Gwamnan na jihar Borno ya buƙace su da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a wata mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng