UTME: Jerin Sunaye da Jihohin Ɗaliban da Suka Yiwa Jarabawar JAMB Cin Kaca a 2024
- Hukumar JAMB ya bayyana sunayen ɗaliban da suka ci maki mafi yawa a jarabawar share fagen shiga jami'a ta bana 2024
- Shugaban JAMB na kasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da sunayen ɗaliban a wurin taron majalisar gudanarwa ta hukumar a Abuja
- Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta yi amai ta lashe kan mafi ƙarancin shekarun shiga jami'a a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami'o'i a Najeriya (JAM) ta saki sakamakon jarabawar da ɗalibai suka zauna a faɗin kasar da wasu ƙasashen waje.
Kamar yadda aka saba a kowace shekara, JAMB ta kuma fitar da jerin ɗaliban da suka nuna hazaƙa da ƙwazo suka samu maki mafi yawa a jarabawar UTME 2024.
Shugaban hukumar JAMB na kasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana ɗaliban da suka suka yiwa jarabawar cin kaca, kamar yadda Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da ministan ilimi, Tahir Mamman ya yi amai ya lashe kan mafi ƙarancin shekarun shiga jami'a a Najeriya
A farko, ministan ya bayyana cewa daga yanzu sai ɗalibi ya cika shekara 18 sannan za a ba shi gurbin karatu a jami'o'in ƙasar nan.
Sai dai nan take masu ruwa da tsaki suka yiwa matakin bore, lamarin ya sa Farfesa Tahir ya janye kalamansa tare da ayyana shekaru 16 a matsayin mafi karancin shiga jami'a.
Sunayen waɗanda suka fi samun makin JAMB
Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana sunayen ɗaliban da suka fi samun makin JAMB da jihohin da suka fito a wurin taron majalissr gudanarwa ta JAMB a Abuja yau Alhamis, Leadership ta rahoto.
Ga su kamar haka:
S/N | Sunaye | Maki | Jiha |
1 | Olowu David | 367 | Ondo |
2 | Alayande David | 367 | Oyo |
3 | Orukpe Joel | 367 | Edo |
4 | Emmanuel Jeremiah | 366 | Akwa Ibom |
5 | Essiet Etini | 365 | Akwa Ibom |
6 | Ezenwoko Zara | 365 | Abia |
7 | Umoh Joshua | 365 | Akwa Ibom |
8 | Mamudu Abdulraham | 364 | Edo |
9 | Adeleke Abdulbasit | 363 | Kwara |
10 | Echem Victor | 363 | Ribas |
11 | Etute Emmanuel | 363 | Edo |
12 | Jedidiah Chidiebube | 363 | Imo |
13 | Adesanya Oluwatimilehin | 363 | Ogun |
JAMB ta gano masu ƙaryar takardu
A wani rahoton kuma kun ji cewa hukumar JAMB ta bayyana gano wasu masu karyar kammala manyan makarantu a Najeriya
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oleyede da ya bayyana haka ya kara da cewa matasa 3000 na rike da shaidar kammala makarantun.
Asali: Legit.ng