Wasu Manyan Malamai Daga Kano da Jihohi 6 Sun Biyo Hanyar Dawo da Zaman Lafiya a Arewa

Wasu Manyan Malamai Daga Kano da Jihohi 6 Sun Biyo Hanyar Dawo da Zaman Lafiya a Arewa

  • Yayin da matasa ke shirin yin zanga-zanga, Malamai akalla 70 sun bi hanyar da suke ganin za ta dawo da zaman lafiya a yankin Arewa
  • Malaman sun taru a jihar Kaduna domin gudanar da addu'o'i kwana ɗaya tare da rokon Allah ya share hawayen al'ummar Arewacin Najeriya
  • Jagoran shirya taron, Malam Lawal Ibrahim BK ya ce sun sanya rundunar sojoji a addu'o'insu domin Allah ya ba su nasara kan ƴan bindiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Kimanin Malaman addinin Musulunci 70 daga sassan Arewa maso Yamma ne suka taru a jihar Kaduna domin gudanar da taron addu’o’i na kwana daya.

Manyan Malaman sun shirya taron addu'o'in ne domin rokon Allah SWT ya dawo da zaman lafiya da ci gaba a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

"A daina alakanta ni da 'yan bindiga": Matawalle ya yi magana kan bidiyon Bello Turji

Taswirar jihar Kaduna.
Manyan Malamai akalla 70 sun yi taron addu'o'in neman zaman lafiya a Arewa
Asali: Original

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Malaman da suka halarci taron addu'o'in neman zaman lafiya sun fito ne daga jihohin Kaduna, Kano, Sakkwato, Jigawa, Zamfara, Kebbi da Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman Arewa sun sa sojoji a addu'a

Malaman sun kuma yi wa babban hafsan tsaron ƙasar nan, Janar Christopher Musa da duka rundunar sojojin Najeriya addu'ar Allah ya ba su nasarar kawar da ƴan bindiga.

Jagoran shirya taron addu’o'in, Malam Lawal Ibrahim BK, ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a yankin.

Malam Lawal ya kuma nuna kwarin guiwa da fatan cewa addu'a za ta dawo da zaman lafiya domin babu abin da ya gagari Allah Mai Girma da Ɗaukaka.

Dalilin shirya taron addu'o'i a Kaduna

 “Mun yanke shawarar gudanar da taron addu’o’i ne ga yankin Arewa maso Yamma saboda yankin na fama matsalolin tsaro da suka hada da ‘yan fashin daji da garkuwa da mutane."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun kashe basarake mai martaba da ɗansa a Arewa

"Mun kuma sanya babban hafsan hafsoshi da sojojin Najeriya cikin addu’o’inmu, muna fatan Allah ya ba su nasara a duk wani kalubalen da suke fuskanta,” in ji Malam Lawal Ibrahim.

Manyan malaman da suka je Kaduna

Manyan Malumman da suka halarci taron sun hada da Sheikh Muhammad Nur daga Katsina sai irinsu Malam Jamilu Ismail daga Kano.

Akwai Malam Rabiu Al-Mustapha daga Sokoto da Malam Kamaludeen Ismail daga Zamfara.

Wani matashin malami a Katsina, Yahuza Abdullah ya shaidawa Legit Hausa cewa mafitar da ta ragewa yan Arewa a yanzu ita ce addu'a.

Ya ce duk da ba ya goyon bayan a shirya taro musamman saboda addu'a amma ya shawarci Musulmi su koma ga Allah, su riba ci lokutan addu'a su kai kukansu ga Allah.

"Wallahi ana cikin yanayi a ƙasar nan musamman Arewa, ni dai bana goyon bayan zanga zanga amma muna da makami mai ƙarfi watau Addu'a, mutane mu koma ga Allah," in ji shi.

Kara karanta wannan

Satar Akuya ta jawo matar aure ta buga wa mijinta gatari, ya mutu nan take

Sheikh Kabiru Gombe ya ba matasa shawara

A wani rahoton kuma Sakataren ƙungiyar Izala, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe ya yi magana kan zanga-zangar da matasa ke shiryawa

Shehin Malamin ya yi kira ga matasa su rungumi zaman lafiya kana su guji duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262