'Yan Bindiga Sun Je Har Gida, Sun Harbe Basarake Har Lahira a Arewa
- Ƴan bindiga sun je har gida sun kashe dagacin kauyen Kurmin-Kare da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna
- Wani mazanin kauyen, Shehu Baba ya bayyana cewa bayan kashe basaraken, ƴan bindigar sun yi awon gaba da mutum uku a harin
- Matasan garin sun yi kukan kura, suka afka wa ƴan bindigar kuma sun yi nasara kama ɗaya daga cikinsu bayan ya faɗo daga kan babur
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindigan daji sun hallaka dagacin kauyen Kurmin- Kare da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna, Ishaya Barnabas.
Ƴan fashin dajin sun harbe basaraken har lahira kana suka yi awon gaba da wasu mutum uku a sabon harin da suka kai a jihar da ke Arewa maso Yamma.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Shehu Baba ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe dagaci a Kaduna
Mutumin ya bayyana cewa ƴan bindigar sun kai farmaki kauyen da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar daren ranar Talata lokacin mutane sun yi nisa a barci.
Shehu Baba ya ce maharan sun shigo garin a kan babura kuma kai tsaye suka nufi gidan dagacin, inda nan take suka harbe shi har lahira.
A cewarsa, bayan kashe basaraken ne kuma ƴan bindigar suka shiga wasu gidajen maƙota, suka yi awon gaba da mutum uku.
Matasa sun kama ɗan bindiga
Ya ci gaba da cewa matasan ƙauyen sun hada kai kuma suka yi nasarar kama daya daga cikin ‘yan fashin bayan ya fado daga kan babur.
Sai dai matasan ba su ɗauki doka a hannunsu ba, sun mikawa dakarun sojoji ɗan bindigar da suka damƙe domin ɗaukar matakin da ya dace.
Har kawo yanzu jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan faruwar lamarin ba.
Yobe: An kama basarake da zargin kisa
A wani rahoton kun ji cewa jami'an ƴan sanda sun kama wani dagaci bisa zargin hannu a kisan direban motar tarakta a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabas.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem ya ce basaraken ya haɗa matasa suka je gona suka yi kisan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng