Kwamishinan Kano Ya Tsallake Rijiya da Baya, Iyalansa 3 Sun Mutu a Gobara

Kwamishinan Kano Ya Tsallake Rijiya da Baya, Iyalansa 3 Sun Mutu a Gobara

  • Gobara ta yi barna mai muni ciki har da rasa rai a gidan kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar Kano, Dakta Yusuf Kofar Mata
  • Rahotanni na nuni da cewa mummunar gobarar ta faru ne a safiyar yau Laraba, 17 ga watan Yuli yayin da mutane ke barci
  • Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Abdullahi Saminu ya tabbatar da faruwar lamarin tare da yin karin haske

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - An samu mummunar gobara a gidan kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano, Dakta Yusuf Kofar Mata.

Rahotanni na nuni da cewa gobarar ta yi barna sosai ciki har da asarar rayuka da dukiya mai yawa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tirela da karamar mota sun yi karo, an yi asarar rayuka

Gobara ta yi barna a Kano
Gobara ta kashe mata a gidan kwamishinan Kano. Hoto: Kabiru Garba
Asali: Facebook

Legit ta gano cewa kwamishinan ya bayyana adadin yan uwansa da gobarar ta tafi da rayuwarsu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe gobarar ta faru?

Jaridar the Guardian ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da safiyar yau Laraba yayin da mutanen gidan ke barci.

Haka zalika an ruwaito cewa gobarar ta faru ne a gidan kwamishinan da ke unguwar Kofar Mata a birnin Kano.

Mutane nawa suka rasu a gobarar?

Kwamishinan ya bayyana cewa mutane uku ne suka rasu a gidansa ciki har da 'yar cikinsa mai suna Maimuna da aka fi sani da Islam.

Bayan haka akwai mata biyu, daya babbar addarsa ce mai suna Hajiya Khadijah sai kuma matar yayansa mai suna Juwairiyya.

Bayanin hukumar kashe gobara

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Abdullahi Saminu ya ce gobarar ta jawo asara sosai amma ba za a iya kididdige asarar ba a lokacin

Kara karanta wannan

Ruwa ya ruguza gidaje da rumbunan abinci a Arewa, mutane sun shiga tasko

Tuni dai aka yi sallar gawar wadanda suka rasu da misalin karfe 11 na safe a Kofar Mata da ke jihar Kano.

Gobara ta tashi a kasuwar Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar Karu da ke babban birnin tarayya Abuja .

An ruwaito cewa gobarar ta kama gadan-gadan yayin da jami'an hukumar kwana-kwana ke iya bakin kokarinsu domin shawo kanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng