Kasafin Kudin 2024 Zai Karu, Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Nemi a Kara Tiriliyoyin Naira

Kasafin Kudin 2024 Zai Karu, Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Nemi a Kara Tiriliyoyin Naira

  • Shugaban kasa ya mika bukatarsa ga majalisa domin amincewa da karin tiriliyoyin Naira a cikin kasafin kudin shekarar 2024
  • A wasikar da shugaba Bola Tinubu ya aika ga majalisar, ya nemi a sahale masa karin Naira Tiriliyan 6.2 a cikin kasafin na bana
  • Idan majalisa ta amince, kasafin kudin 2024 zai karu zuwa Naira Tiriliyan 33.7 daga Naira Tiriliyan 27.5 da aka riga aka yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mika bukatarsa ga majalisa domin sahale masa kara Naira Tiriliyan 6.2 a kasafin kudin 2024.

Bukatar na kunshe cikin wasikar da shugaban ya aika majalisa wanda Godswill Akpabio ya karanta, inda ake neman karin a kan Naira Tiriliyan 27.5 na kasafin.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya nemi karin Naira Tiriliyan 6.2 Tiriliyoyin Naira a Kasafin Kudi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Za a kara kasafin kudin 2024

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Bola Tinubu ya nemi a dauki Naira Tiriliyan 3.2 daga cikin asusun kudin shiga domin gudanar da manyan ayyuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma shugaban ya nemi a sake ware Naira Tiriliyan 3 domin ayyukan gudanarwa na shekarar nan.

Sauran bukatun Tinubu ga majalisa

Karin bukatun da shugaban kasa, Bola Tinubu ya aika ga majalisa sun hada da yiwa dokar kudi ta shekarar 2023 gyaran fuska da zai bayar da damar dora haraji ga bankuna.

Jaridar The Cable ta wallafa cewa tuni aka bayyana bukatun guda biyu na shugaban domin ba su kulawar gaggawa.

Idan har majalisa ta amince da bukatun Tinubu, kasafin kudin kasar nan zai karu zuwa Naira Tiriliyan 33.7 daga Naira Tiriliyan 27.5 da shugaban ya rattaba wa hannu a ranar 1 Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu za su dauki mataki kan Sanata Ali Ndume bisa sukar shugaban kasa

Kasafin kudi: An tsige shugaba saboda cushe

A baya mun ruwaito cewa kansiloli a karamar hukumar Egor da ke jihar Edo sun tsige shugaban yankin bisa zargin cushe a kasafin kudi da sauran zarge-zarge.

Baya ga cushe a kasafin, majalisar karamar hukumar na zargin Eghe Ogbemudia da sauran laifuffuka da su ka jibanci cin hanci da rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.