Nade Naden Tinubu: APC Ta Kwantar da Hankalin Arewa, Ta Yi Albishir ga Masu Jiran Mukamai
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fito ta kare shugaban ƙasa Bola Tinubu kan rabon muƙaman da yake yi a gwamnatinsa
- APC ta bayyana cewa Shugaba Tinubu na ƙoƙarin ganin ya yi adalci domin ganin kowane yanki ya samu muƙami mai gwabi
- Jam'iyyar dai na yin martani ne kan ƙorafe-ƙorafen da wasu mutanen yankin Arewacin Najeriya ke yi kan cewa an bar yankin a baya wajen ba da muƙamai masu tsoka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi adalci ga kowane yanki na ƙasar nan a manyan muƙaman da ya raba a gwamnatinsa.
Jam'iyyar na martani ne kan ƙorafe-ƙorafen da wasu jiga-jigan yankin Arewacin Najeriya ke yi na cewa ba a ba yankin muƙamai masu gwaɓi ba.
Da yake zantawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' ranar Talata, sakataren yaɗa labarai na APC, Felix Morka ya ce shugaban ƙasan na ƙoƙari wajen ganin ya yi adalci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me APC ta ce kan naɗe-naɗen Tinubu?
Kakakin na APC ya bayyana cewa masu sukar naɗe-naɗen na Shugaba Tinubu sun yi gaggawa domin akwai sauran waɗanda za a yi nan gaba.
"Shugaba Tinubu yana ƙoƙarin yin adalci, akwai adalci a manyan muƙaman da ya raba."
"Wannan gwamanatin shekara ɗaya kawai ta yi a kan mulki, ba ta gama raba muƙamai ba har yanzu. Akwai sauran ofisoshi da dama da ba a cike su ba. Akwai sauran muƙaman da za a raba."
"Muna da shugaban ƙasa, muna da mataimakin shugaba ƙasa. Muna da fannin tsaro, muna da fannin kuɗi."
"Mafi yawan ma'aikatan fannin tsaro sun fito ne daga Arewacin Najeriya yayin da ministan kuɗi da gwamnan CBN suka fito daga Kudancin Najeriya."
- Felix Morka
Tinubu ya ba jami'an tsaro wani umarni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ba babban hafsan tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa umarnin daƙile satar mai da fasa bututun mai a yankin Niger Delta cikin ƙanƙanin lokaci.
Shugaba Tinubu ya ce wannan ɓarnar ta zama matsalar da ta shafi ƙasar da ya kamata a kawo ƙarshenta domin bunƙasa haƙo mai a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng