An Shiga Jimami Bayan Tirela da Karamar Mota Sun Yi Karo, An Yi Asarar Rayuka

An Shiga Jimami Bayan Tirela da Karamar Mota Sun Yi Karo, An Yi Asarar Rayuka

  • Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar mummunan hadarin mota da ya salwantar da rayuka da dama
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adam ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a jiya Talata
  • Haka zalika, DSP Lawal Shiisu Adam ya kuma bayyana yadda mummunan haɗarin ya faru tare da faɗin dalilin aukuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar haɗarin mota da ya lakume rayuka.

Rahotanni na nuni da cewa haɗarin ya faru ne a jiya Talata, 16 ga watan Yulin shekarar 2024 a hanyar kasuwar Kanya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wuta kan matafiya, sun yi awon gaba da mutane da yawa

Hadarin mota
Hadarin mota ya salwanta rayuka a Jigawa. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan ne cikin sakon da DSP Lawal Shiisu ya rattaba hannu a kai kamar yadda rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane nawa suka rasu a haɗarin?

Kakakin rundunar yan sanda a jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ya bayyana cewa mutane 14 ne suka mutu a haɗarin.

Har ila yau, DSP Lawal Shiisu Adam ya bayyana cewa a yanzu haka akwai mutane hudu da ke kwance a asibiti, rahoton Daily Trust.

Me ya kawo haɗarin motar?

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa jami'an hukumar shige da fice sun tsayar da babbar mota kirar tirela a shinge domin bincike.

Ana cikin haka ne sai wata karamar mota kirar Toyota ta nufo shingen da gudu kuma aka tsayar da ita, amma matukin ya ki tsayawa.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Jagaban, wani ɗan majalisar tarayya daga Kaduna ya mutu

Tirela da karamar mota sun yi karo

A kokarin matukin ƙaramar motar na canza hanya ya gudu ne sai ya yi karo da wani bangare na babbar motar kuma ya jawo asarar rayuka 14.

Rundunar yan sanda ya bayyana cewa a yanzu haka ana gudanar da bincike domin ganin matakin da ya kamata a dauka.

An yi hadarin mota a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa haɗarin mota ya yi sanadin mutuwar mutane 12 yayin da wasu 28 suka ji raunuka daban-daban a kan babban titin Zariya zuwa Kano.

Hukumar kiyaye haɗurra ta jihar Kaduna (FRSC) ta ce tsere da gudun da ya wuce ƙima ne suka haddasa faruwar lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng