Badakalar N80bn: Yahaya Bello Ya Gabatar da Wata Bukata a Gaban Kotu

Badakalar N80bn: Yahaya Bello Ya Gabatar da Wata Bukata a Gaban Kotu

  • Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya sake miƙa kokensa a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja
  • Bello wanda ke fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC kan badaƙalar N80bn ya buƙaci kotun ta ɗage sauraron shari'ar har sai baba ta gani
  • Ya kuma buƙaci kotun da ta janye umarnin da ta bayar na cafke shi har zuwa lokacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukunci kan ƙarar da ya shigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sake gabatar da sabuwar buƙata a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Yahaya Bello ya buƙaci babbar kotun da ta ɗage ci gaba da sauraron shari'ar da hukumar EFCC ta shigar a kansa har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Ana batun zanga zanga, Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro wani umarni

Yahaya Bello na so a dage shari'arsa da EFCC
Yahaya Bello ya bukaci kotu ta dage shari'arsa da EFCC Hoto: Alhaji Yahaya Bello, EFCC
Asali: Facebook

Wace buƙata Yahaya Bello ya nema?

Ya kuma buƙaci kotun da ta janye umarnin cafke shi, har zuwa lokacin da kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci kan ƙarar da ya ɗaukaka, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buƙatun na Yahaya Bello na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da lauyansa, Musa Yakubu (SAN) ya rubuta, rahoton jaridar Businessday ya tabbatar.

Wasiƙar mai ɗauke kwanan ranar 12 ga watan Yuli kuma an aika da ita zuwa ga alkalin kotun, mai shari'a Emeka Nwite, gabanin gurfanar da tsohon gwamnan da za a yi a ranar Laraba, 17 ga watan Yuli.

Hukumar EFCC dai tana tuhumar Yahaya Bello da laifin karkatar da Naira biliyan 80.

Yahaya Bello na tsoron kamu

Amma, a ƙarar da ya daukaka kan shari’ar da ake yi masa, Yahaya Bello ya nuna fargaba kan makomarsa idan har aka ci gaba da shari’ar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ba gwamnan PDP shawara kan 'yancin kananan hukumomi

A cikin ƙarar da ya ɗaukaka mai lamba CA/ABJ/CR/535/2024, tsohon gwamnan ya buƙaci a jingine umarnin cafke shi wanda ya ce an bayar ba bisa ƙa'ida ba a ranar 17 ga watan Afrilu, 2024.

Ya kuma buƙaci a mayar da takardar ƙarar zuwa ga babban alƙalin babbar kotun tarayya, domin a ba wani alƙali jan ragamar shari'ar.

Karanta wasu labaran kan shari'ar Yahaya Bello

Kotu ta yi fatali da buƙatar Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa alƙalin babbar kotun tarayya, mai shari’a John Tsoho, ya ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Yahaya Bello da EFCC daga Abuja zuwa jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Sukar Shugaba Tinubu ta jawo sanatan Arewa na fuskantar barazana a zaben 2027

Hukumar EFCC na neman ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban kuliya bisa zargin ya karkatar da N80.2bn, inda tsohon gwamnan na jihar Kogi ya nemi a mayar da shari'ar zuwa Kogi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng