Wata sabuwa: Gwamnatin Kano Ta Sake Bankado Yadda Ganduje Ya Wawure Dukiyar Jihar
- Gwamnatin jihar Kano ta sake zargin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da yin watanda da dukiyar jihar
- Gwamnatin na zargin Ganduje da tsohon kwamishinan shari'a na jihar da haɗa baki wajen karkatar da N240m kan wata shari'a
- A cikin ƙarar wacce aka shigar a gaban babbar kotun jihar Kano, gwamnatin ta ce ta shirya shaidu huɗu waɗanda za su tabbatar da zargin da take yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sake shigar da sababbin tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin tana zarginsa da kashe kuɗaɗen jihar Naira miliyan 240 domin gudanar da wata shari’a ta ƙashin kansa.
Gwamnatin Kano ta yi ƙarar Ganduje
Jaridar The Punch ta ce tuhumar mai lamba K/143c/24, an shigar da ita a gaban babbar kotun jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar na jihar, Musa Abdullahi, ya shigo cikin tuhumar a matsayin wanda ake ƙara na biyu.
Laifukan da ake tuhumarsu sun haɗa da haɗa baki domin aikata laifuka, cin amana da cin hanci da rashawa, waɗanda suka cancanci hukunci a ƙarƙashin dokokin jihar Kano, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
A cikin tuhume-tuhumen, gwamnatin jihar karƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta yi zargin cewa Ganduje da tsohon kwamishinan sun haɗa baki wajen aikata rashin gaskiya.
Wace tuhuma ake yiwa Ganduje?
Gwamnatin na tuhumarsu da haɗa baki wajen karkatar da N240m domin gudanar da wata shari'a wanda hakan ya jawo asara ga gwamnati da al'ummar jihar Kano.
Ana zarginsu da fitar da kuɗin ne kan wata shari'ar ma'aikatan gwamnatin Kano waɗanda EFCC ke bincika, yayin da a zahiri an fitar da kuɗin ne domin samun umarnin kotu na hana EFCC bincikar Ganduje.
Gwamnatin a cikin ƙarar ta ce ta shirya gabatar da shaidu guda huɗu waɗanda za su bayar da hujjoji kan zargin da take.
Kotun dai ba ta sanya ranar fara sauraron shari'ar ba.
Gwamnatin Kano ta yi ƙarar tsohon kwamishina
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano a ta shigar da karar tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, tare da wasu kan zargin waskar da N24bn na kananan hukumomi.
Murtala Sule Garo ya kasance kwamishina ne har sau biyu a ma'aikatar ƙananan hukumomi karkashin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Legit.ng